Kotun Ƙoli: Lauyoyi sama da 200 sun lashi takobin mara wa Gwamnan Kano baya

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla sama da lauyoyi 200 masu zaman kansu daga Arewa ne suka bayyana ƙudirinsu na taimaka wa Gwamna Abba Kabir na Jihar Kano domin ganin ya yi nasara a Kotun Ƙoli bayan ɗaukaka ƙara da ya yi.

Lauyoyin ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Abba Kabir Yusuf Volunteer Lawyers Forum For The 19 Northern states And Abuja, sun bayyana aniyarsu ta mara wa Gwamna Abba baya ne a taron manema labarai da suka shirya a Arewa House ranar Lahadi a Kaduna.

Mai magana da yawun lauyoyin, Yusuf Ibrahim, sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Kotun Ƙoli kan kada su bari tsarin mulkin ya zama mai gudana ƙarƙashin jam’iyya guda, yana mai cewa, “hakan ba shi da alfanu ga tsarin dimokuraɗiyya.”

Lauyoyin sun ce dole ne a bi tsarin dokar ƙasa don tabbatar da ƙuri’ar kowane ɗan Nijeriya ya yi tasiri.

Sun ƙara da cewa, a bayyane yake hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke cike yake da kura-kurai, don haka suka yanke shawarar mara wa Gwamna Yusuf baya ɗari-ɗari a Koton Ƙoli.