Kotun Ƙoli ta amince da soke rajistar jam’iyyun siyasa 22

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun Ƙoli ta amince da hukuncin soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa 22 da Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi a shekarun baya. Jam’iyyu 22 na daga cikin 74 da INEC ta soke rajistarsu a 2020 sakamakon rashin taɓuka abin a zo a gani a zaɓen 2019.

Mai Shari’a Ejembi Eko na Kotun Ƙoli ya yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke, wanda ya ƙalubalanci matsayar INEC na soke rajistar jam’iyyun. Mai Shari’a Eko ya bayyana cewa, Kotun Ɗaukaka Ƙara a karan kanta ta taɓo batun rashin sauraron shari’ar adalci ga ɓangaren jam’iyyun 22 da aka soke, inda ta cimma matsaya ba tare da jin ta bakin wasu ɓangarori a kan lamarin ba.

“Wannan buƙata da INEC ta nema ya dace kuma an amince da hakan. Hukuncin kotun da ke ƙasa an yi watsi da shi,” cewar Ejembi.

Kotun ƙolin ta bayyana cewa kotun ɗaukaka ƙara ta fitar da batun sauraron ƙarar ne daga duban buƙatar ɗaukaka ƙara da jam’iyyun siyasa suka shigar, amma ta ƙi yin abin da ya dace, domin yin adalci ga wasu da lamarin ya shafa.

INEC dai ta ce ta soke rajistar jam’iyyun siyasa 74 ne saboda rashin samun nasarar lashe kujera ko ɗaya na siyasa a babban zaɓen da ya gabata na 2019.