Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da ba a yi wa Jokolo adalci ba a sarautar Sarkin Gwandu

A ranar Litinin, Kotun ɗaukaka Ƙara da ke Sokoto ta sake tabbatar da hukuncin kotun ƙasa a kan korar tsohon Sarkin Gwandu, Al-Mustapha Jokolo, tana mai cewa gwamnatin Jihar Kebbi ba ta ba shi damar kare kansa ba yadda ya kamata.

A cikin hukuncin da aka yanke baki ɗaya, wanda Mai Shari’a Ebiowei Tobi ya karanta, kotun ta bayyana cewa ɗaukaka ƙarar da Gwamnatin Kebbi ta gabatar ba ta da tushe, kuma ta tabbatar da hukuncin kotun ƙasa.

Tobi ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan nazari mai zurfi kan hukuncin kotun ƙasa.

Kotun ta nuna rashin bin ka’idar dokar naɗa sarakuna da korar su ta Jihar Kebbi.

“In na dubi hukuncin kotun ƙasa, ba ta ambaci hujjojin da ke zama tushen hukuncin ba. Ɗaukaka ƙarar ba ta da tushe don haka an kore ta. Don haka, na tabbatar da hukuncin kotun ƙasa da aka bayar,” in ji shi.

Ya ce ɗaukaka ƙarar da ta shafi wannan batun duk an yi hukuncin su ne a matsayin ɗaya kuma duk sun kasance a kan wannan batu.

Majiyoyi sun tabbatar cewa Gwamnatin Kebbi tare da wasu mutane 12 ne suka ɗaukaka Ƙara kan hukuncin kotun ƙasa da ya ba da daman kare hakkin tsohon sarkin.

A yayin shari’ar, Lauyan masu daukar kara, Mr Yakubu Maikyau (SAN), ya wakilci masu ɗaukaka ƙarar, yayin da Lauyan wanda ake ƙara, Mr Fascal Onyenobi, ya wakilce shi.

A watan Afrilun 2016, Kotun ɗaukaka Ƙara ƙarƙashin Mai Shari’a Tunde Awotoye ta tabbatar da hukuncin Kotun Ƙoli, tana mai bayyana cewa matakin Gwamna ya saɓa da tanadin Sashe na 6 da 7 na dokar naɗa sarakuna da Korar su.