Kotun Birtaniya ta ƙi amincewa da belin Ekweremadu da matarsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kotun majistare na Uxbridge da ke ƙasar Birtaniya ta ƙi bayar da ba da belin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice kan zarginsu da safarar mutane da kuma sassan jiki.

’Yan sanda sun kama mutanen biyu ne a ranar Alhamis a birnin Landan.

An tattaro cewa, waɗanda ake zarginsu da hannu a lamarin wani yaro ne mai shekaru 15 da haihuwa wanda Ekweremadu da matarsa suka kawo shi ƙasar Birtaniya daga kan titin Legas a Nijeriya.

An tsare su a hannun ’yan sanda a ƙasar Birtaniya.

An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 7 ga Yuli, 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *