Kotun Kano ta ɗaure ɓarawon yara shekara 104 a kurkuku

Daga AMINA YUSUF ALI

A Juma’ar da ta gabata Babbabar Kotun Kano ta 2, ta yanke wa Paul Owne hukuncin zaman kurkuku na shekara 104 bisa laifin kitsa sace wasu yara a jihar.

Alƙalin kotun, Jastis Zuwaira Yusuf ita ce ta yanke hukuncin haka, tare da ba da umarnin garƙame Paul ba tare da wani zaɓin biyan tara ba.

Haka nan, duk da yanke masa hukuncin zama a gidan gyaran hali, kotun ta kuma buƙaci Paul ya biya kuɗi har N100,000 kafin a jefa shi kurkuku.

Paul dai ya amsa aikata laifuffuka 38 da lauyan mai gabatar da ƙara ya tuhume shi da aikatawa.

Yayin da shi kuwa lauya mai kare Paul bai yi wani musu ba kan hukuncin da kotun ta yanke.

Paul ya haɗa baki da wasu mutum biyar ne wajen sace wasu yara ‘yan ƙasa da shekara 10 daga Kano inda suka kai su su Anacan jihar Anambra suka sayar.

An gurfanar da Paul ne tare da abokan harƙallarsa da suka haɗa da Ogbono Emmanuel da Igwe Loise da Duru Monica da Oracha Chinelo da kuma Ifedigwe.

Sai dai su ɗin sun ƙi amincewa da aikata laifukan da aka tuhume su da aikatawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *