Kowa ya ci buzu…

Daga IBRAHIM YAYA

A kwanakin baya ne wasu kafofin watsa labaran Amurka suka ruwaito wani rahoton da cibiyar bincike ta Pew ta gudanar dake nuna cewa, kimanin kashi 77 cikin 100 na Amurkawa baƙaƙen fata, sun bayyana cewa, ya kamata zuriyar mutanen da aka bautar a tarihin ƙasar, a biya su diyya.

Sai dai kuma, a cewar rahoton yawancin waɗanda aka zanta da su, ba sa tunanin cewa, za a biya baƙaƙen fatan diyyar, ko da yake, ƙungiyoyin ƙabilu da wasu Amurkawa sun dade suna fatan ganin hakan ya tabbata.

Sannu-sannu aka ce ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba.

Kuma kowa ya ci buzu, ai dole ya yi aman gashi.

Cibiyar bincike ta Pew ta bayyana a cikin rahoton nata cewa, gaba daya, baligai baƙaƙen fata, ba su da tabbacin game da yiwuwar biyan diyyar, amma da dama daga cikinsu, sun bayyana cewa, ya kamata gwamnatin tarayyar Amurka, ta ɗauki nauyin biyan diyyar baki ɗaya ko kaso mafi yawa daga ciki.

Haka kuma kimanin kashi 45 cikin 100 na Amurkawa baƙaƙen fata, sun ce da wuya a samu daidaito.

Bugu da ƙari, kusan mutum 9 cikin 10 na baligai baƙaƙen fata, suna son ganin an yi gyaran fuska ga ɓangarorin kotuna da sauran sassan tsarin shari’ar manyan laifuffuka.

Gabanin wannan rahoto, shugaba Joe Biden na Amurka, ya bayyana a ranar 20 ga watan Augusta da aka ware a matsayin ranar tunawa da cinikin bayi a Amurka cewa, sama da shekaru 400 da suka gabata, an tilasta kai wasu bayi 20 daga nahiyar Afrika zuwa gabar ruwan da yanzu ake kira Amurka.

Daga bisani an sace tare da sayar da miliyoyi, cikin ɗaruruwan shekarun da suka biyo baya, wani ɓangare na tsarin cinikin bayi dake zaman asalin laifin ƙasar Amurka.

Duk da kiraye-kiraye da wani rukuni na al’umma ke yi na neman haƙƙinsu game da cin zalin da aka yi musu, har yanzu ana ci gaba da ganin mummunan tasirin wannan tarihi a Amurka, ciki har da nuna kyama da wariyar launin fata, da tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba wanda har yanzu ya yi muni a ƙasar.

Koma dai mene ne, kamata ya yi Amurka ta nemi gafara tare da biyan diyya ga waɗanda ta take musu hakki. Masu iya magana dai na cewa, a juri zuwa rafi, wata rana za a fasa Tulu.