Koyi da irin taimakon ƙasar Sin zai haifar da zaman lafiya a duniya

Daga FA’IZA MUSTAPHA

A jiya ne aka gudanar da taro na 60 na hukumar raya duniya ta MDD, inda zaunanen wakilin ƙasar Sin a majalisar, Zhang Jun ya gabatar da shawarwarin tabbatar da fatattakar talauci da wadatar abinci. Kamar yadda kowa ya sani, ƙasar Sin ta riga ta yi adabo da talauci tun a ƙarshen shekarar 2020, don haka, a ganina, babu wadda ta dace da bada shawara kan yadda za a yaƙi talauci a duniya kamar ƙasar Sin ko kuma jami’anta.

Kamar yadda Zhang Jun ya bayyana yayin taron na jiya, annobar COVID-19 ta kawo koma baya kan nasarorin da duniya ta samu wajen fatattakar talauci tare da jefa mutane kusan miliyan 800 cikin matsalar yunwa.

Haƙiƙa, ƙasashe masu tasowa na cikin mawuyacin hali, musamman a yankin ƙahon Afrika dake fama da fari, haka zalika mutane masu rauni na ƙara shiga tasku. Kamar yadda ya ce, shugaban ƙasar Sin ya gabatar da wata shawara ta kafa “Rukunin Ƙasashe Abokai Masu Rajin Tabbatar da Cigaba a Duniya (GDI)” a watan Junairun da ya gabata. Idan da manyan ƙasashe za su riƙa ajiye son zuciya da neman iko, su riƙa tunani da hangen nesa irin na ƙasar Sin, da yanzu duniya ta samu ci gaba fiye da yadda ake tsammani.

Wannan shawara ta GDI da shugaban ƙasar Sin ya gabatar da zummar taimakawa ƙasashe masu tasowa, lallai ta zo a lokacin da ake buƙatarta. Sai dai, ƙasar Sin ita kaɗai ba za ta iya biyan buƙatun dukkan ƙasashe ba, ya zama wajibi ƙasashen da suka nuna sha’awa, suka kuma amince da shawarar, su ma su bada tasu gudunmuwa komai ƙanƙantarta. Misali, a Litinin da ta gabata, ƙasar Sin ta yi nasarar kammala aikinta na bayar da tallafin abinci ga ƙasar Kenya, ɗaya daga cikin ƙasashen dake yankin ƙahon Afrika. Tun cikin shekarar 2018, Sin ɗin ta ƙaddamnar aikin, inda ta kasa shi cikin rukunoni 8.

A gaskiya, ana buƙatar irin wannan yunƙuri daga sauran manyan ƙasashen duniya domin irin wannan namijin ƙoƙari ne ya sa ƙasashe masu tasowa ke ƙara amincewa da ƙasar Sin tare da yaba mata ainun. Ai wanda ya taimake ka a lokacin da kake tsananin buaata, shi ne amini na ƙwarai. Na yi imanin cewa, al’ummar Kenya da ma sauran ƙasashen da Sin take taimakawa a irin wannan lokaci, ba za su taɓa mantawa da alherinta ba. Haka zalika, idan ƙasashen duniya suka yi koyi da wannan yunƙuri, to zai haifar da sakamako mai ɗimbin alfanu a nan gaba, kamar fahimta da girmamawa da mutunci har ma da zaman lafiya, inda a ƙarshe za a cimma dunƙulewar duniya da samun kyakkyawar makoma ga kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *