Koyon girki ba wai ga yaya mata kawai ya kamata ya tsaya ba, har da maza- Fatima Gwadabe

*An wuce lokacin bawa mata shawarar su nemi sana’a saboda abu ne da yake a fili – Fatima Gwadabe

Fatima Gwadabe suna ne da ya karaɗe ƙasar nan musamman a wajen mata da ke kallon tashar Arewa24, domin kuwa Fatima Rabiu Gwadabe ƙwararriya ce da ta ke koyar da girki irin na Afirka, na Turawa da na gargajiya. Fatima Gwadabe ta shekara 3 ta na koyar da girke-girke daban-daban a tashar Arewa24, kuma ta samu kyautuka masu yawa a wannan ɓangare. A hirar ta da wakilinmu a Kano za ku ji tarihinta da kuma yadda shirin ya samo asali:

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Za mu so ki gabatar mana da kan ki ga masu karatun mu?
Sunana Fatima Rabiu Gwadabe. An haife ni a garin Kano, na yi karatun Islamiyya da na boko duk a Kano. Na karanci fannin aikin Jarida wato ‘Mass Communication’ a Jami’ar Bayero ta Kano. Ta fannin girki kuma na yi kwasa-kwasai a fannoni daban-daban, kamar su haɗa lemuka, sarrafa fulawa, girke-girken gida da na ƙetare da sauransu.

Ta yaya ki ka samu kanki a tashar Arewa24?
Akwai abokiyar aikina Nafisa Abdulkarim mai gabatar da shirin Tauraruwa a da, ita ta turomin a lokacin Arewa24 suna neman gurbin ‘reporter/researcher’, na yi ‘applying’ aka kira ni ‘interview, na samu nasara. Na fara aiki da Arewa24 a matsayin ‘reporter/researcher’ a sashin Gari Ya Waye.

Kina gabatar da shiri mai suna ‘Akushi da rufi’ a tashar Arewa24. Me ake nufi da Akushi da rufi?
Duk da dai ba ni na ƙirƙiri sunan shirin ba, kasancewar ba ni na fara gabatar da shirin ba. Akushi Da Rufi sai Sarki shi ne kirarin da ake yi wa akushi duba da darajarsa da kuma yadda yake alkinta abinci wajen hana shi gumi, lalacewa da wari da kuma kasancewa cikin ɗumi koyaushe, wato dai yana a matsayin ‘food flask’ duk da dai shi daga itace ake sassaƙa shi, kuma ya na ɗaukan tsawon lokaci bai lalace ba. Ta ɓangaren lafiya kuma ya na da ‘anti cancer properties, anyi duba da waɗannan abubuwan wajen samar wa da shirin suna.

Yaushe ki ka fara gabatar da shirin?
Shekaru uku kenan da na fara gabatar da shirin.

Me shirin ya ƙunsa?
Shirin ya ƙunshi girke girke na zamani da na gargajiya, girke girkenmu na gida da na ƙasashen waje. Hanyoyi da dabarun sarrafa kayan abinci, koyar da girki a sauƙaƙe masu ƙara lafiya, ƙawata abinci da sauransu.

Ya zuwa yanzu kwalliya na biyan kuɗin sabulu kuwa akan yadda ake kallon shirin?
Alhamdu lillah, kwalliya ta biya kuɗin sabulu, ta na kan biya a kodayaushe, duba da saƙonnin godiya da adduoi da muke samu daga ɓangarori daban daban.

Waɗanne nasarori za ki iya cewa kin samu daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu?
Nasarori ba za su ƙirgu ba, sai dai godiyar Allah a kowanni lokaci. Babbar nasara a wajena a kowane lokaci shi ne; yadda mutane suke bin shirin, kuma suna gwada irin abubuwan da muke koyarwa, suna turo mana.
Na samu ‘award’ da aka karramani a matsayin ‘Best Cooking Show Presenter of the Year’ daga wata ƙungiya mai suna ‘SUNARS Global Concept a Jihar Zamfara. Haka zalika shawarwari na yadda shirin zai ƙara ƙawatuwa da yabo da nake samu daga wajen masu kallo shi ma nasara ce.


Baƙi maza da mata da suke tururuwar shigowa cikin shirin shi ma nasara ce a koyadaushe. Ba zan manta kuma da yara da nake samun sakonninsu ta waya, wasu ta ‘video’ iyayensu na turomin suma suna gwada girke-girke, wasu suna cewa su ma sun zama Fatima Gwadabe Akushi Da Rufi, ina jin daɗin hakan sosai. Zan yi amfani da wannan dama na yi godiya ga kowa da kowa, Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya ƙara zumunci, amin.

Wane irin ƙalubale ki ke fuskanta wajen gabatar da shirin Akushi da rufi?
Rayuwa ma dama gabaɗaya cike take da ƙalubale, ƙalubale nan da can ba a rasashi, amma dai ina kallonshi a matsayin abu mai zuwa ya wuce. Abinda zan iya cewa ƙalubale a kodayaushe wanda ko gobe ma zai iya faruwa duk da dai a yanzu ya zama tarihi, shi ne wasu lokutan baƙo ko baƙuwar da muke gayyata wani uzurin kan hanasu zuwa, wasu kuma basa sanarwa sai lokaci ya ƙure.

A wasu lokutan za ki ga wasu matan bayan sun yi aure sai ki ga ana samun saɓani wajen iya girki. Daga ina matsalar ta ke?
Matsalar rashin iya girki ba wai matan aure kaɗai ta shafa ba, har da ‘yan mata, matsalar kuma daga tushe daban daban ne, wata matsalar ƙiyuwa ce da son jiki daga wajen mata, wata kuma daga ɓangaren iyaye ne basa koyawa yayansu, duk da dai ni ina raayin koyar girki ba wai ga yaya mata kawai ya kamata ya tsaya ba, har maza suma ya kamata su iya saboda gudun ɓacin rana. Shawara dai ‘yanmata da matan aure su dage su koyi girke ko yaya ne, su kuma maza koda an samu matsala uwargida bata iya ba, akwai hanyoyi da dama da za a iya bi wajen ganin ta koya ba tare da tashin hankali ba, masu iya magana ma na cewa da koyo akan iya.

Yaya ki ke kallon macen da take zaune babu sana’a?
Toh, ni a yanzu sai nake ganin kamar an wuce lokacin bawa mata shawarar su nemi sana’a, saboda abu ne da yake a fili yanzu alfanun da neman na kai yake da shi. Sana’a maganin zaman banza, sanaa huce haushi, sana’a rufin asiri.

Fatima a bakin aiki

Ya batun aure fa?
Ba ni da aure, sai jiran lokaci.

Wane irin kalar kaya ki ka fi so?
Ina son doguwar riga, walau abaya, atamfa da dai sauransu. Sannan ina son kaloli masu haske.

Abinci fa wanne ki ka fi so?
Abinci ina son tuwo, shinkafa da kuma kayan ganye.

Wane kira za ki yi ga mata masu bibiyar ki da kuma waɗanda ke son ƙwarewa a iya kirki?
‘Nothing comes easy inji Bature, ba wai girki kaɗai ba, komai ma idan kana son iyawa sai ka jajirce. Kiran da zanyi gare su shi ne; su dage, su jajirce kuma su nemi sanin ilimin abin daga wajen masana, don gabaɗayan mu kullum muma koyo muke da neman ilimi, daga lokacin daka saka a ranka ka iya, za a wuce a barka a baya. Ya kamata koyaushe ka zama cikin bibiyar abinda ke tafiya da zamani.

Mene ne burin ki a rayuwa?
Burina a rayuwa dai alhmadu lillah Allah ya cika min ɗaya daga cikin burikana, na son yin suna akan aikina. Sauran kuma Allah ya tabbatar da su, amin.

Mun gode
Ina godiya matuƙa.