KSCB ta ƙaddamar da kwamitin mutane 10 kan gasar rubutun da ta shirya 

Daga AISHA ASAS 

A wata sanarwar da ta fito daga hannun Abdullahi Sani Sulaiman, Jami’in Watsa Labarai na Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano, ta bayyana shiri na musamman da hukumar ke yi wurin ganin ta gudanar da gasar rubutun da ta saka a makon da ya gabata, don ganin gasar ta samu tsari da nasarar da ake fatan samu.

Da wannan ne Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano,  Alhaji Abba El- mustapha ya ƙaddamar da kwamitin mutane 10 da za su bayar da gudunmuwa a gudanar da gasar rubutun Hausa mai zuwa, wadda ta kasance irin ta ta farko da hukumar ta shirya tun kafuwar ta.

Da yake ƙaddamar da kwamitin a ɗakin taro na hukumar, Alhaji Abba El- mustapha,  ya bai wa kwamitin wuƙa da nama kan dukkan ayyukan gasar tun daga farko har ƙarshe. Ya kuma buƙaci babban goyon bayansu da haɗin kai domin cimma burin da aka sa gaba.

Mambobin kwamitin su ne:

1 Farfesa Ahmad Magaji (BUK)

2 Dakta Halima A Dangambo (BUK)

3 Malam Kamilu Dahiru Gwammaja (BUK)

4 Malam Ado Ahmad gidan Dabino

5 Fauziyya D Sulaiman

6 Dan’azumi Baba cheɗiyar yan gurasa

7 Hajiya Balaraba Ramat

8 Abubakar Zakari G/Babba

9 Isah Abdullahi Haruna

10 Iliyasu Garba.

Abba El- mustapha ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya bai wa kwamitin hikima da jajircewa wajen gudanar da aikin tare da yi wa ’yan takarar fatan samun nasara a gasar ba tare da wata matsala ba.

Da take jawabi a lokacin da take ƙaddamar da kwamitin, Dakta Halima A Dangambo daga sashen harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero, Kano, ta nuna sha’awar jami’ar na son haɗa kai da hukumar tace finafinai ta Jihar Kano a gasar da nufin samun sakamako mai kyau.