Kuɗaɗen Ibori da aka maido mallakar jihar Delta ne – Majalisa

Daga WAKILINMU

Majalisar Wakilai ta Ƙasa, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta maida kuɗaɗen da Ibori ya sata, Pan milyan  £4.2, ga Jihar Delta.


Wannan ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisar daga jihar Delta suka gabatar wa majalisar ne a Larabar da ta gabata.

Haka nan, ‘yan majalisar sun ce jimillar kuɗin Pan miliyan £6.2 ne amma ba milyan  £4.2 ba kamar yadda aka ruwaito.

Bugu da ƙari, Majalisar ta buƙaci Ma’aikatar Kuɗi ta Kasa da ta bai wa Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, umarnin ya miƙa wa Majalisar dukkan takardun da ke da alaƙa da batun kuɗaɗen.