Kuɗin makamai: Majalisar Wakilai ta gayyaci Attahiru da Emefiele

Daga FATUHU MUSTAPHA

Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta buƙaci Hafsan Hafsoshi, Lieutenant General Ibrahim Attahiru da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, da su bayyana a gaban wani kwamitinta ya zuwa watan gobe.

Kwamitin Majalisar ƙarƙashin shugabancin Hon Olaide Akinremi, ya gayyaci waɗanda lamarin ya shafa ne a Litinin da ta gabata bayan da suka ƙi amsa masa gayyatar farko da ya yi musu.

Hon Bede Eke shi ne wanda ya gabatar da ƙudirin a gayyato mutum biyun zuwa gaban Majalisar, wanda ya nuna ɓacin ransa kan rashin amsa gayyatar kwamitin majalisar a baya.

‘Yan majalisar mambobi ne a kwamitin da ke bincike kan sha’anin sayen makamai, aiki da su, yadda ake mu’amala da su, yanayin amfani da alburusai da makamantansu, a tsakanin sojoji da dangoginsu a Nijeriya.

Tun farko, an gayyaci Attahiru da Emefiele ne don amsa wa majalisar tambayoyi kan batun sayen makamai amma sai suka ƙi amsa gayyatar, lamarin da ‘yan majalisar suka yi tir da shi.

Daga nan, sai ‘yan majalisar suka sake ɗaukar matakin gayyatar Attahiru da Emefiele don su bayyana a gabansu ya zuwa ranar 7 ga Afrilu, 2021.

A baya-bayan nan, akwai batun zargin cewa wasu maƙudan kuɗaɗe da aka ware don sayo makamai sun ɓace a ƙarkashi shugabancin tsoffin shugabannin fannin tsaro.