Kuɗin namiji ba shi ne ya kamata mace ta yi tinƙaho da shi ba – Raihan Ƙamshi

“Idan har kasuwanci ka ke son yi sosai, sai ka soke bayar da bashi”

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A yanzu dai za a iya cewa mata sun farka daga zaman rashin sana’a da a ke ganin an bar su a baya musamman a Ƙasar Hausa ta yadda a baya a ke yi wa matan yankin kallon koma baya a fagen kasuwanci da dana’a.

Raihan Imam Ahmad wadda aka fi sani da Raihan Imam (Ƙamshi) ta na ɗaya daga cikin matasan mata da suke gudanar da harkokin kasuwancin su, kuma a yanzu ta kai matakin zama babbar ‘yar kasuwa a vangaren kayayyakin ado da kwalliya na mata.

Domin yadda tarihin kasuwancin ta da kuma hanyoyin da ta bi har zuwa lokacin da ta zama babbar ‘yar kasuwa. Wakilinmu ya tattauna da ita, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance;

MANHAJA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.

RAIHAN ƘAMSHI: To ni dai sunana Raihan Ahmad Imam wadda aka fi sani da Raihan Ƙamshi. Kuma tarihin rayuwata, ni haifaffiyar garin Kano ce, a nan na tashi na girma, kuma duk wasu abubuwa na rayuwa da abin da ya shafi karatuna duk a nan Kano na yi su.

To a matsayin ki ta ‘yar kasuwa, masu karatu za su so jin irin kasuwancin da ki ke gudanarwa.

E to Alhamdulillahi, ni na tashi ne da yanayi na kasuwanci tun ma ban kai haka ba, ni mace ce mai son sana’a komai ƙanƙantar ta kuwa. Saboda yadda nake son sana’a, hakan ta sa tun ba ni da shago na ke sayo kayayyaki nake sayarwa a gida, har ta kai ta kawo kuma Alhamdulillahi Allah ya dafa mini a cikin nema na, na zo na samu na buɗe shago nake zuba kayana a ciki nake sayarwa.

Kayan da ki ke sayarwa waɗanne kalar kaya ne?

Ai ni kasuwancina ko’ina akarada ce ta kowanne ɓangare, don zan iya fita waje na sayo kayayyaki, zan kuma iya sayen wasu a nan gida, waɗanda in sun ba ni sha’awa kuma nake ganin zan samu ƙaruwa a cikin su, zan iya sayen su na sayar, kuma ni daman abin da na fi shahara aka sanni da shi, shi ne, sayar da kayan mata, kamar su kayan sakawa kamar takalma jakunkuna, sarƙoƙi da sauran kayan ado na mata, don haka a yanzu kamar yadda nake faɗa maka ina da waje da na buɗe a nan Kano a Zoo Road, kuma a yanzu ma hakan muna ta shirin yadda za mu buɗe wani wajen nan gaba kaɗan wanda a nan ne zan mayar da hankali na na zauna sosai, saboda ko kafin na Zoo Road na yi wani wajen a nan hanyar BUK Kano da ke Kofar Famfo, kuma baya ga sayar da kayan da a ke yi, ana yin gyaran jiki da gyaran gashi a wajen.

Ita wannan harkar a na ganin wata harka ce mai cike da sirri, ko ya ya abin yake?

To ai ita harkar kasuwanci kowacce idan mutum ya iya ta, akwai sirri a cikin ta, don haka kowacce harkar tana da sirrin.

Ya ya harkar gwagwarmayar tafiyar da kasuwanci take irin naki, musamman ga mace?

E gaskiya ne akwai gwagwarmaya, domin ka san duk wani abu da za ka nema a yanzu ka yi shi a matsayin sana’a, to sai ka sha gwagwarmaya a cikin sa. Akwai abubuwa da dama, amma shi kasuwanci daman haquri a ke yi. Ba zai yiwu yau ka buɓe kasuwa ka ce sai ka ga yadda ka ke so a lokaci guda ba. Saboda za ka iya yin sati nawa ba a sayi abu ba, don haka idan aka samu mai gajin haquri, sai ya ga abin ya ƙi tafiya yadda yake so, sai ya haƙura. To amma ita sirrin sana’a idan har ka yarda ka saka a ranka za ka iya wannan gwagwarmayar da a ke yi ta yau da gobe, to wata rana fa za ka sha mamaki.

Abin da ya shafi tafiye -tafiye a kasuwanci shi ma wani ƙalubale ne mai zaman kansa ga mata, ya ki ke tunkarar lamarin?

E aiki ne. Amma ka san shi neman kuɗi babu inda ba ya kai mutum, kuma kuɗin nan daman su muke nema, don haka ba za ka ce kullum za ka rinƙa dogara a jikin wasu ba. To idan har ka sa a ranka neman za ka yi ko, to duk yadda za a yi sai ka daure da wahalar da za a sha. Ni a yanzu nan na taƙaice maka a iya Najeriyar nan idan na shiga Legas zan sayo kayayyaki, idan ka ganni ba za ka ce ni ba ce, saboda gaske nake yi, don haka harkar kasuwamci sai an jajirce, don haka duk wanda zai yi harkar kasuwanci ba ma mace ba, to sai ya tashi tsaye.

A yanzu harkar kasuwancin ki, iya Legas ki ke zuwa sayen kaya ko har kina fita ƙasashen waje?

Ai na faɗa maka ni akarada ce, komai ma ina yi, don haka a ko’ina ina yin sayayya ta. Don yanzu za ka iya gani na je Saudiyya na sayo kaya, wanda na san idan na kawo su nan za a saya. Za ka iya gani na je Dubai, nan ma zan ƙara sayo kayan da nake ganin zan zo na sayar da su a nan. Sannan kuma idan aka dawo nan gida Najeriya, gaskiya in dai sayayya ta tashi ko wani abu, ba ya wuce Legas sai Kwatano.

To a yanzu da ki ka yi ƙarfi ki na zuba kaya ne a shago a zo a saya, ko ga ‘yan kasuwa ki ke rabawa su haɗa miki kuɗinki?

A’a ban kai ƙarfin diloli ba, ina sayo kaya ne na zuba su a wajen da nake harkar kaauwanci na, wasu na ajiye su a gida, wasu kuma kafin ma su zo an sayar da su, a na kawowa zan bi kowa na ba shi nasa.

A yanzu kasuwanci ya zama ɓangare biyu, akwai wanda za zuba a wajen kasuwancin a zo a saya, sai kuma na onlayin, a wanne ki ka fi bayar da ƙarfi?

To ni dai gaskiya na fi gane na kawo kaya na ajiye su na sayar da su. Amma ta onlayin abin da ya sa shi ma ba zan ce ba na yi ba, wasu da yawa su na gani na ta onlayin saboda sun san cewa ni ‘yar kasuwa ce, sai su yi mini magana na tura musu.

To ko akwai matsalolin da a ke samu a kasuwancin onlayin?

E ba zan ce babu ba, amma dai ya danganta. Idan Allah ya haɗa ka da irin masu matsala dole za ka samu kanka a cikin matsala. Idan kuma Allah ya taimake ka da na arziki babu wata matsala a ciki, amma dai wanda na fi bada ƙarfi a kansa, shi ne, na ajiye, mai buƙata ya zo ya saya.

A matsayin ki ta mace, mai ya fi burge ki a harkar kasuwancin ki?

To ni abin da yake yi mini daɗi kuma ya fi burge ni shi ne idan aka zo ɓangaren gyaran gashi. Saboda ni ina da son gyaran gashi, don haka ban ƙi a ce kullum za a wanke mini kaina a gyara mini shi ba, don haka harkar gyaran gashi na ma buɗe ta ne saboda karan kaina. Shagona akwai kayayyaki kamar yadda na faɗa maka, amma sai da aka samar da ɓangaren gyaran gashi wanda na yi hakan ne ko a yi ciniki ko kada a yi, ni dai in dai zan rinqa zuwa ana yi mini gyaran gashina, to buƙata ta biya, don haka harkar tana burge ni.

Idan mace tana son ta zama ‘yar kasuwa, waɗanne hanyoyin ya kamata ta bi?

Hanyar kawai ita ce ta saka zuciyarta ta na son ta zama ‘yar kasuwa, kuma ya zamo tana da jarinta haka, sai ta fara ko da kaɗan-kaɗan ne ta gwada ta gani kasuwancin da ta fara ya karɓe ta. To idan ta fara da kaɗan sai ka ga ta zo ta zama wani abu, don haka sai an kula an raini jarin, don an ce idan ka ji wane ba banza ba. Duk wanda ka ga yana jin daɗin sa a harkar kasuwanci, idan aka nuna maka wahalar da ya sha a baya, to kai da kanka sai ka tausaya masa.

Wanne ƙalubale ne ki ka tava fuskanta a kasuwanci da ba za ki taɓa mantawa da shi ba?

To akwai su kuwa sosai, saboda kamar yadda na faɗa maka ita harkar kasuwanci sai an yi haƙuri, to haka abin yake, kuma sannan yanzu rayuwa ta zama abin da ta zama. Za ka ga mutane wani kawai zai ga kasuwancin ku ne ya zo daya sai ka ga yana kullata, irin masu zuciya da tsatsa za ka ga ransu yana kullata ba sa jin daɗi, wani ma ya rinƙa yi maka hassada, ko abu za a saya wajenka sai ya rinƙa nunawa ba haka ba, to duk irin waɗannan abubuwan mun gan su. Sai kuma irin mutane masu son zuciya wanda haka za ka ga su kawai ƙoƙarin su su karya ka. Sai mutum ya zo ya sayi kayanka saboda kawai wata manufa da yake da ita, sai ya yi tafiyar sa ya ƙi biya kuma ka yi ta bin sa ya ba ka kuɗin ya hana ka, to wannan shi ma ƙalubale ne.

To amma idan har kasuwancin ka ke so ka yi sosai, sai ka soke bayar da bashi a cikin harkar ka, saboda sun iya karya mutum daga mazan har matan. Don kwanaki akwai wata qawata da ta zo ta karvi kayana, amma maganar da nake maka har yanzu ba ta biya ni ba, kuma ba mu ƙara haɗuwa da ita ba ko a waya ba ta yi mini magana.

Don haka ina kira ga mata musamman waɗanda ba su damu da su yi kasuwanci ba, su tashi su nemi sana’a saboda kuɗin namiji ba shi ne ya kamata a ce mace ta na tunƙaho da shi ba. Har kullum ki zama ke ma da kafafuwanki ki ke a tsaye kina yin sana’ar ki, saboda ko su mazan idan suka ganki da sana’a kin fi mutunci a idon su,saboda idan ya ganki ba ki da sana’a duk son da yake yi miki zai fara jin tsoron yanzu idan na ce ina son wannan shikenan na zama bankinta komai ni zan yi mata duk da idan ya yi ba laifi ba ne. Wannan ga wadda ba ta da aure kenan.

kuma ita mace ‘yar a tausaya mata ce saboda ita ce a qasa amma idan akwai wata sana’a da ki ke juya kuɗin kafin ki faɗa masa ma kin yi da kan ki. Don haka ina kira ga mata na gidan aure da ma waɗanda ba su yi ba, da su tashi su yi sana’a, domin ita ce darajar su da ƙimar su a wajen mazajen su.

To madalla mun gode.

Ni ma na gode sosai.