Kuɗi sun zama zuciyar komai na rayuwa – Hajara Idris Dambatta

“Ilimin ’ya mace na al’umma ne”

Daga ABUBAKAR M. TAHIR

Mai karatu wannan tattaunawa ce da Manhaja ta yi da Hajiya Hajara Idris Dambatta, shugabar haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan mata da suka kammala makarantar kwana ta Malam Madori (MADOGSAJ). A cikin zantawar, ta kawo irin namijin ƙoƙarin da gidauniyar haɗaɗɗiyar ƙungiyar ta yi wajen haɗa kan ‘yan ƙungiyar gami da ƙoƙarin da suke na wayar da kan iyaye kan muhimmancin ilimin ‘ya’ya mata. Haka kuma ta kawo fafutukar da suka yi na ƙirƙirar asusun wata-wata, wanda suke gudanar da ayyukan ƙungiyar. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Ko za ki gabatar da kanki ga masu karatu?
HAJIYA HAJARA: Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.Ni dai sunana Hajara Idris Dan Batta. An haifeni a garin Maiduguri na Jihar Borno. Bayan an yi wa yayar mahaifinmu aure, an kai ta garin Dan Batta da ke Jihar Kano, wannan ta sa mahaifinmu ya ba ta ni, mu ka tafi can. Bayan zuwanmu Dan Batta, sai ta sani a wata marantar firamare da ake kira da Barde ‘Primary School’. Bayan kammala firamare, na samu damar tafiya makarantar kwana da ke garin Malam Madori, inda na yi qaramar sakandare da babbar. Na kammala a shekarar 1989, shekaru 33 da suka gabata. Bayan kammala karatun sakandare da kwanaki arba’in da uku, dama na samu miji a aka min aure. Yanzu haka ina da ‘ya’ya biyar, ɗaya ya rasu, saura huɗu.

Bayan sakandare ba ki ci gaba kenan?
Eh, maganar gaskiya na yi ta ƙoƙarin na ci gaba da karatu, sai ya zama maigidana ba ya so. Wannan ta sa mahaifana suka buƙaci inyi biyayya na haƙura. Amma alhamdu lillah, yanzu haka ilimin da mu ka samu ya taimaka mana wajen harkokin kasuwanci na cikin gida da kuma zamantakewar yau da kullum a tsakanin mu da abokan zamanmu.

Kin kasance ɗaya daga cikin shuwagabannin ƙungiyar tsofaffin ɗalibai ta makarantar kwana ta Malam Madori. Shin yaushe kuka ƙirƙiri ƙungiyar?
Eh to, maganar gaskiya shine, mun ƙirƙiri haɗaɗɗiyar ƙungiyar (MADOGSAJ) sama da shekaru ashirin, wanda kuma ta ƙunshi aji na farko har ya zuwa aji na ƙarshe, wato waɗanda suka kammala a shekarar 2021.

Mene ne ya ja hankalin ku har kuka ƙirƙiri wannan tafiyar?
To alhamdu lillah, gaskiyar magana, babban abinda ya ja hankalin mu, mu ka buɗe wannan qungiyar shi ne, ganin yadda makarantar ta ke fama da matsalolin rashin guraben tsugunno, da kuma lalacewar Masallacin makaranta, wanda yake shafar rayuwar yaran mata. Haka kuma munyi la’akari da cewa, su ‘yan ƙungiya mu na da ƙarancin haɗin kai, wannan ta sa sakamakon wannan ƙungiya yanzu haka dukka membobin mu kanmu a haɗe yake, kasan tsarin ‘boarding school’ na girmamawa, har yanzu indai kaga ‘senior’ ɗinka kana kiranta Anty, ita ma tana baka girmanka, wannan ta sa mu ka fara wannan aikin, kuma alhamdu lillah zuwa yanzu za mu ce kwalliya tana biyan kuɗin sabulu.

Waɗanne nasarori ne za a iya cewa kun samu a wannan tafiya?
To alhamdu lillah, nasarori ba za su ƙirgu ba, saboda yawansu, amma abu mafi muhimmanci da mu ke jin daɗinsa, maganar haɗin kan nan. Sannan mun gudanar da taruka har guda uku, wanda biyu a Kano, sai kuma babban taron da mu ka gabatar kwanakin baya a cikin makarantar, wanda kusan dukkanin membobinmu sun samu halarta, yara da manya. Sannan daga cikin nasarorin, mun samu damar gyara Masallacin da ke cikin ‘hostel’, mun samu Masallacin ya lalace ba ma a iya salla sosai a cikinsa, saboda rashin kyau, amma mu ka gyara shi. Aqalla mun kashe kuɗi Naira miliyan ɗaya da dubu dari ɗaya. Sannan kusan mun lura da wata babbar matsala da ke damun yara, kasancewarsu ‘yan mata, duk wanda ya san mace ya santa da saurin kamuwa da cuta mai yaɗuwa, sai mu ka lura yaran ba su da matsuguni mai kyau, sukan shiga jeji, su gudanar da buƙatarsu, wannan ta sa mu ka gina mu su banɗakai kusan guda uku a nan harabar makaranta, wanda shima aqalla ya ci kuɗi sama da Naira dubu ɗari huɗu da ɗoriya. Haka kuma mun yi ma ɗaya daga cikin ‘ya’yan membarmu da Allah ya mata rasuwa kayan ɗaki, wanda haƙiƙa danginta sun ji daɗin wannan tallafi da mu ka ba su. So gaskiya dai nasarorin suna nan birjik, sai dai mu zayyana waɗannan.

To da yake kowanne abu ba ya tafiya sai da kuɗi. yaya kuke samar da kuɗaɗen tafiyar da ƙungiya?
To, alhamdu lillah, kamar yadda ka faɗa, kuɗi ya zama zuciyar komai a yanzu, babu wani abu da zai gudana ba tare da kuɗi ba. Haka kuma babu wata tafiya da zata ɗore matuƙar babu hanyoyin samun kuɗi. A wannan ƙungiya mu na da wani tsari, wanda da shi ne mu ke gudanar da komai, mu kan bada kuɗin wata wanda kowacce memba ta ke bayarwa, hakan ta sa mu ka tara kuɗin da mu ka yi wanccan aiki na miliyan da ɗoriya,
Kuma haƙiƙa membobinmu suna da ƙoƙari wajen bayarwa, shi ne ya sa mu ke ta faɗin cewa mun samu haɗin kai wanda ya fi ƙarfin a misalta shi.

Ya zuwa yanzu, a ‘yan ƙungiyarku kun samu waɗanda suka taka wasu muhimman matakai na rayuwa?
To, wannan maganar gaskiya saidai mu yi wa Ubangiji godiya, ya zuwa yanzu mun samu manyan ma’aikatan gwamnati, ‘yan siyasa, manya ‘yan kasuwa da malaman makarantu waɗanda mu ke alfahari da su. Mu kan haɗu gabaɗaya, kowa ya kawo gudunmawa da yake da ita domin samar da cigaba. Wanccan yana da ilimi a kan kaza, wanccan kaza haka mu ke haɗuwa mu tada abu wanda zai amfanar da tafiyar ta mu.

Mene ne babban burinku a wannan tafiyar? 
To, gaskiya babban burinmu, bai wuce a ce yau ga shi mun samar da wasu fitattun mutane a faɗin ƙasar nan ba. Ina nufin a ce yau ga wata kwamishina ko minista wanda ta kammala makarantar Malam Madori. Duk wanda ya san makarantar kwana, yasan ana koyon karatu gami da tarbiyya, wannan ta sa mu ke samun fitattun mutane. Haka kuma muna burin a ce yau duk shekara mukan yi wani aiki na musamman ga makarantar domin ingantawa tare da farfaɗo da daraja da mutuncita a idon duniya.

Wane kira ki ke da shi ga iyaye wajen barin ‘ya’yansu zuwa makarantar kwana?
Eh, wannan duk wanda ya sani, ya san cewa, makarantar kwana ba wai karatu kawai ake koyarwa ba, ana bada tarbiyya, misali ka ɗauki yara guda biyu a gida ɗaya, ɗaya ya je ‘boarding’, ɗaya bai je ba, za ka tarar wanda ya je ‘boarding’ ya fi hankali, tarbiyya nutsuwa da sanin ya kamata. Haka kuma iyaye mu sani, shi ilimin ‘ya mace al’umma gabaɗaya yake amfana, domin za ta haihu ta kuma samar wa da yaranta tarbiyya ta gari. Haka kuma iyaye su sani, yanzu lokacin da za mu ba wa yaranmu dama ne su yi karatu saboda duniyar ta koma komai sai da ilimi.

Wane kira kike da shi ga shugabanni wajen tallafa wa irin wannan tafiya taku?
To kiran da ake da shi ga shuwagabannin mu shine; su taimaka, su dubi irin wannan ƙoƙari na gina al’umma. Babban burinmu shi ne, gina al’umma, su daure, su cika ma na alƙawarin da suka mana, su kuma zuba jari a wannan harka ta ilimintar da ‘yan mata, haka su ma ‘yan kasuwarmu da masu hannu da shunin mu, mu na kai ƙoƙon baranmu gare su, su tallafa mana.

Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.