Ku amsa waɗannan tambayoyi kafin ku yanke hukuncin rabuwa

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da haɗuwa a wannan makon! Sannunku da jimirin karatun jaridar Manhaja! A wannan makon za mu yi magana a kan yadda wasu lokuta a rayuwar aure da zaman yake yin zafi ya ƙi daɗi. Har ma su yanke shawarar su rabu da juna. Ko ɗaya ya dinga riyawa a zuciyarsa ba mafita illa ya rabu da ita ko ita ta dinga tunanin idan ba ta rabu da shi ba ba ta da sauran wani ‘yanci. Eh haka ne, akwai wasu lokuta na rayuwar aure da suke zuwa ku ji sam ba kwa jin daɗin zaman.

Amma sai dai wasu lokutan ma’aurata kan yanke hukuncin rabuwa da halin da suke ciki ba tare da tunanin me zai je ya zo ba. Kawai gani ake daga an rabun, kowa zai cigaba da rayuwarsa yadda yaje so. Sai dai wani sa’in ma sai an yi rabuwar ake gane cewa, an fita daga wani ƙangin ne kawai an faɗa makamancinsa ko wanda ma ya fi shi illa. Duk da mun san namiji ke da ragamar rabuwar aure amma mace ma tana da nata tasirin. Idan ta so rabuwa da miji takan uzzura masa iya uzzurawa da tayar masa da hankali. Ko ma dai yaya ne, kafin ku yanke wancan hukuncin na rabuwa, ku fara tunawa da waɗannan abubuwa:

Abu na farko shi ne, kun shirya rabuwar? Na san me karatu zai ce, wanne shiri kuma? Eh ita ma rabuwar aure tana buƙatar zurfin tunani da hangen nesa da shiri kafin a yi ta. In dai har za mu yi shirye-shiryen aure kafin ya zo, ko kuma haihuwa, ko ritayar aiki da sauransu, me zai hana shi ma rabuwar a yi mata shiri a tsara yadda za a yi. Domin idan ma ba ku sani ba, ku sani, akwai wata rayuwar bayan rabuwa. A nan za a samu damar yanke hukuncin ya dace a rabu ko a’a?

Shirye-shiryen sun haɗa da idan ke mace ce, wanne shiri kike da shi na dogaro da kanki na yadda za ki kula da yaranki da kanki bayan kin rabu da mijinki wanda yake kula da ke da su? Wanda zan aura shin zai yadda na je masa da yara gidansa? Idan ya yarda shin mahaifin yaran zai yarda na je masa da yara wani gidan? Idan ya yarda wa zai ɗauki dawainiyarsu ta yau da kullum? Idan na mai da su gidansu wa zai rike min su? Idan na kashe auren, haka zan dauwama ba aure ba don na kula da yarana? Kai kuma namiji, ka shirya rayuwa ba mace? Ka san dai idan yau ka rabu da matarka ba gobe zaka sake sabon aure ba ko? To wanne tanadi ka yi wa wannan lokacin? Idan kuna da yara, ka shirya riƙe su ko kuwa ita za ka bar wa? Idan ta ce ba za ta riƙe su ba, kana da mai riƙe maka su?

Na biyu, Me ya sa ka zaɓe ta? Me ya sa kika zaɓe shi? Ya kamata ma’aurata duk lokacin da rai ya ɓaci su dinga tuna baya a kan abokin rayuwarsu. Yawan tunasar da kai dalilin da ya sa tun farko kika zaɓe shi a cikin dubban samarinki kika zaɓi rayuwa da shi, ko kai dalilin da ya sa ka zaɓe ta bayan ga dubban mata nan yana ƙara muku ganin girma da ƙimar juna. Shin idan an rabun, za ka samu tamkarta wacce za ta cike gurbinta? Ke za ki samu kamarsa idan kin rabu da shi?

Meye haƙiƙanin dalilin da ya sa kuke son rabuwa? Shin dalilan da suka sa kuke son rabuwa suna da ƙarfi kuwa? Sun kai ƙarfin a rabu ɗin saboda su? Kuma matsalar a kai ne ko a aboki ko abokiyar zama? Ku tsaya ku fahimci haka da kyau. Abinda ya sa yake da muhimmanci ku yi wa kanku wannan tambayar shi ne, kada a je a rabun a sake haɗuwa da wannan dai matsalar a aure na gaba.

Kuna tuna zaman aure ibada ne? Ya kamata idan ana fuskantar matsala a cikin gidan aure a dinga tunawa cewa, zaman aure fa zama ne na ibada da ma ba na jin daɗi ɗari bisa ɗari ba ne. Duk da dai da ma akwai matsalolin da dole sai an yi rabuwar shi ya sa ma Allah ya halatta rabuwar aure duk da yana ƙin ta sosai. Amma abubuwa da yawa da an yi haƙuri masu wucewa ne.

Yayanku: Kamar yadda na faɗa a baya, yaranku abin dubawa ne. Ku dinga la’akari da su yayin yanke duk wani hukunci a rayuwar aurenku. Domin su ma suna matuƙar muhimmanci sannan su ma wani ɓangare ne na jikinku wanda ya kamata ku duba. Domin ‘ya’ya suna tagayyara sosai bayan rabuwar iyayensu. Haka iyaye suna rasa kulawar ‘ya’yansu bayan rabuwa. Ba ma a zancen ƙaranci tarbiyya. Sai an yi da gaske ake samun yara idan sun girma su ji ƙan iyayen da ba su shaƙu da su sosai ba. Ku kuma iyayen a dai-dai wannan lokacin kuka fi buƙatar jin ƙan yaran nasu. Saboda a lokacin girma ya cim ma iyayen yaran.

Al’umma: Me aal’umma za su ce? Ya kamata ku duba al’umma wanne kallo za su yi muku. Mace ko namiji idan suka fiye aure-aure, al’umma suna ɗaukarsu marasa sanin ya kamata. Ko marasa haƙuri. Yi ƙoƙari ku yi haƙuri ku zama mutanen kirki a idon al’umma ta hanyar riƙo da aure.

Iyaye/magabata: Kun shawarce su? Su iyaye da magabata suna hango ku abinda ba ku hango ba. Don haka, ku bi umarninsu a kan biyayyar aure. Ko ba alkhairi, Allah zai iya juyarwa ya kawo alkhairi. Kuma ba a ce su suke zaune da matar ba, kuma sakin ba a hannunsu yake ba, amma idan ka tashi rabuwa da matar ba laifi idan ka shawarce su. Na tabbatar za su iya ba ka shawarar da ta dace.

Zaman tare kuttun zuma ne da madaci. An san dai idan an yi aure ana son zaman lafiya amma haƙiƙanin gaskiya ba kullum ake kwana a gado ba. Dole akwai saɓani manya da ƙanana da zasu dinga shigowa. Saboda haka, wasu matsalolin ba su yi girman a ce an rabu don su ba. Idan miji ko mata suna son rabuwa saboda wata matsala, ya kamata a auna matsalar a gani. Matsalar ba mai gyaruwa ba ce? Ta isa ku rabu saboda ita? To a nan za ku fuskanci me matsalar take aininhin buƙata. Rabuwa ko sasanci? Wata matsalar gyara tare buƙata ta hanyar addu’a ko sasantawa, ko a zauna a tattauna a fahimci juna don kauce da-na-sani bayan rabuwar.

Masu shirin su ga bayan auren: Akwai shaidanun mutane da aljanu waɗanda za su yi ta ƙoƙarin ganin bayan aurenku. Ku kuna nan, su kuma suna can sun wasa takobi don ganin sun datse igiyar aurenku. Wasu ma har zuga suke yi don iza wutar. Ku lura da irin waɗannan. Ku haɗa hannu ku tunkari matsalolinku. Babu auren da ba shi da matsaloli sai dai ma’auratan su yi muku rufa-rufa. Ko kuma tsanannin haƙuri da tawakkalin ma’auratan ya hana su bayyana matsalar ku gani. Idan da dukka ma’aurata za su san haka, da sun huta wa ransu.

Har yanzu ina son ta/son sa? Kafin ku yanke hukuncin rabuwa ku fara yi wa kanku wannan tambaya, don kauce wa da-na-sani a rayuwar gaba. Idan dai da ɓurɓushin son aboki ko abokiyar rayuwa, kuma matsalar auren za ta iya sulhuntuwa me zai sa dole sai an rabu? Shi ya sa wani lokacin bayan rabuwa miji ko mata su yi ta kishin hauka a kan junansu bayan ba igiyar aure a tsakaninsu. Ka ga miji yana kishi da mijin tsohuwar matarsa, haka ita ma ta dinga raɓe-raɓe na son dawowa gidan mijin da ta takura sai an sake ta ta fita. Ko ta yi wani auren ta kasa son mijin kamar mijinta na baya.

Shi ma kuma namijin hakan na iya faruwa a kansa. Anya ba son zuciya? Idan ma’aurata suna son rabuwa, su tsarkake niyyarsu. Za su rabu ne don Allah ba wai don wani abu ba. Ko kuma don sakin ya zama dole. Wata matar takan uzzura miji ya sake ta saboda talauci ko kuma ta hango wani da take so fiye da shi. Ki sani irin wannan zalunci ne kuma nan gaba za ki girbi abinda kika shuka Duniya da lahira.

Haka maza ma sun yi ƙaurin suna a wannan fagen. Namiji kan saki mace saboda wata lalura wacce ta same ta a hannunsa. Haka namiji kan iya sakin mace don ta tsufa. Haka idan yana da mata hu]u yakan rabu da wata don kawai ya samu sararin da zai auro wata da ya hango. Kai ma ka sani wannan abin na ka yi yana nan yana bibiyar ka. Za ka amshi sakamakon aikinka a Duniya da lahira. Allah ya kiyashe mu.

Fushi ne ya haddasa maka son rabuwar? Wasu ma’auratan suna rabuwa da juna cikin fushi ne kuma daga baya a zo ana nadama. Shi mutum idan ya yi fushi idonsa kan rufe ruf ya faɗi abubuwan da a zahiri ba haka yake ba. Don haka, idan za a rabu, a rabu ba don fushi ba. Don fushi dole ƙarshensa nadama.

A nan zan tsaya. Mu haɗu a mako na gaba. Muna godiya da maraba ga masu kiran waya don ba mu shawara ko tsokaci ko addu’a. Haƙiƙs ku ne kuke daɗa ƙarfafa min gwiwa. Na gode.