Ku biya kuɗin hayar ƙasa ko ku rasa kadarorinku – Wike ga masu filaye a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi kira ga masu filaye a faɗin birnin da su biya duk wani kuɗin ƙa’idar mallakar fili da ake bin su ko kuma su rasa su.

Wike ya yi kiran ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da aikin hanyar rukunin bincike ta sojoji da ke Ushafa a ƙaramar hukumar Bwari a ranar Litinin.

Minista Wike ya bayyana kuɗaɗen ƙa’idar a matsayin masu muhimmanci ga samar da ababen more rayuwa da ci-gaba wa birnin, don haka ya ce har ya wallafa sunayen waɗanda ake bi bashi a jaridu, ya na mai cewa da kuɗaɗen ne ya ke aikin titinan Abuja.

Ya yi kira ga mazauna da su kasance masu bada gudunmawa ga ci-gaban birnin ta hanyar sauke nauyinsu wanda yin hakan shi zai ba su damar tuhumar gwamnati idan ba ta yi abin da ya ke alhaki ne akanta ba.