Ku guji sayar da motocinku ɗauke da lamba – gargaɗin FRSC ’yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta gargaɗi ’yan Nijeriya da su guji sayar da motocinsu ɗauke da lamba.

Sabuwar shugabar hukumar a Jihar Ribas, Elizabeth Akinlade ce ta yi wannan gargaɗi yayin ziyarar da ta kai cibiyar ‘yan jarida reshen Jihar Ribas da ke Calabar, babban birnin jihar.

Elizabeth ta ce an yi wannan gargaɗi ne domin kare mutane daga sayar da abuwan hawansu ga mutanen da ba su dace ba ko ɓata-gari.

Ta ci gaba da cewa, mai asalin motar za a kama a duk lokacin da aka yi amfani da motar da ya saida wa wani wajen aikata wani babban laifi.

Ta ƙara da cewa, hukumar na da rumbun bayanai na masu abubuwan hawa, don haka ta ce a duk lokacin da aka sayar da wata mota akwai buƙatar a sauya bayanan mallaka daidai da na wanda aka sayar wa motar.

“Kada ku sayar da motarku ɗauke da lamba (plate number), saboda bayanan da muke da su suna nuni ne da asalin mai motar har da adireshinsa.

“Idan aka yi amfani da motar wajen aikata babban laifi bayan an sayar da ita, maiyiwuwa a tsare asalin mai motar tun da bayanansa ne ke wurinmu, ko da kuwa bai san da laifin da aka aikata ba,” in ji Elizabeth.