Ku jure zafin ƙarancin Naira don zai wuce – Roƙon Buhari ga ’yan Nijeriya

*An bankaɗo Naira Tiriliyan 2.1 da aka ɓoye

Daga AMINA YUSUF ALI
 
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana adadin yawan Nairorin da aka ɓoye waɗanda gwamnatinsa ta bankaɗo tun da CBN ya fara dokar canjin fasalin takardun Naira a Nijeriya. Sannan kuma ya roƙi ‘yan Nijeriya a kan su zama masu haƙurin jure wahalhalun da dokar ta samar.

A cewar Buhari, gwamnaninsa ta samu nasarar bankaɗo aƙalla Naira tiriliyan 2.1 aka ɓoye ba a bankuna ba. Tun daga lokacin da gwamnatin ta sanya dokar sauya fasalin kuɗi. 

Shugaban ƙasar ya yi wannan jawabi a ranar Alhamis ɗin 16 ga watan Fabrairu, 2023 a yayin da yake ba da sanarwa ga kafatanin al’ummar Nijeriya.

Buhari ya ƙara da cewa, duk da dai akwai ƙalubalai da aka samu, amma akwai alfanu sosai a tsarin.

“Na samu rahoto daga majiya mai tushe cewa daga fara wannan tsarin zuwa yanzu an samu nasarar dawo da aƙalla tiriliyan 2.1 da suke a wajen bankuna”. A cewar sa. 

Buhari ya ƙara da cewa, waɗannan alƙalumma na tiriliyan 2.1 su ne kaso 80 na dukkan kuɗaɗen.

Sannan a cewarsa wani ƙarin alfanu na  wannan tsarin ya haɗa da rage matsin tattalin arzikin ƙasa, raguwar aikata ɓarna, wanda zai rage cin hanci da rashawa da arzurta kai ta mugayen hanyoyi. Inji shi. 

Sannan wani alfanun ya haɗa da dadaita farashin canjin kuɗi, samun rance cikin sauqi rage kuɗin ruwa da sauransu. 

Buhari ya bayyana mamakinsa da takaicinsa ga wasu al’amura da wasu ɓata-garin ma’aikatan bankuna suke gudanarwa, shugaban ya ce dole ne a yi musu hukunci.

Sannan ya bayyana cewa, ba wai ba ya sane ne da dukkan halin da alummar Nijeriya suke ciki ba ne. Musamman ma bankuna da suke abubuwan da ba su kamata ba.

Ya ce abin yana masa ciwo kima yana jajentawa ‘yan Nijeriya. Yana fata abubuwa su daidaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *