Ku kasance cikin shirin ƙarin haraji – Ministar Kuɗi ta gargaɗi ‘yan Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Ministar Kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta Nijeriya, Hajiya Zainab Ahmad ta gargaɗi ‘yan ƙasar a kan su kasance cikin shirin samun ƙarin haraji.

A cewarta, ba makawa za a samu ƙarin haraji a kan wasu mutane da wasu sana’o’i a wannan matsakaicin zangon. 

Ministar ta bayyana haka ne ga ‘yan kasuwa yayin gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a a game da kasafin kuɗi na shekarar 2021 ranar Litinin ɗin da ta gabata a Abuja. Hajiya Zainab ta ƙara da cewa, Gwamnatin tana tunanin ƙarin harajin ne domin neman farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan.

Shi dai wannan taron jin ra’ayoyin jama’ar kwamitin kuɗi na majalisar wakilai shi ne ya tsara shi.

Ministar ta bayyana cewa, a yanzu haka dai an nemi yin gyare-gyare da garambawul da dama a kan dokokin 2021 da suka shafi kuɗi, haka kuma ana sa ran za a ƙara yin wasu gyare-gyare nan da tsakiyar shekara ta 2022.

 “Waɗannan gyare-gyare da kwaskwarima ana sa ran ba makawa za su jawo ƙaruwar haraji a kan wasu mutane da sana’o’i da kamfanoni a Nijeriya”. Inji ta. 

Yanzu da a cewar ta nan da tsakiyar 2022 za a yi ƙoƙarin samar da wasu sabbin dokokin da suka shafi harkar kuɗi. Domin a cewar ta, akwai wasu dokoki da suke tauye gwamnati haƙƙin samun kuɗin haraji kai-tsaye. Su ma duk za a yi musu garambawul. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *