Ku kira ni da ‘Malam Dikko Raɗɗa’ maimakon ‘Your Excellency’ – Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, ya bayyana dalilin da ya sa ba ya so a kira shi da kalmar ban girma, wato ‘Your Excellency’ bayan an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar.

Raɗɗa ya bayyana cewar ba ya son a kira shi da ‘Yallaɓai har zuwa ƙarshen wa’adin mulkinsa da zai fara ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

“Ba na son a kira ni ‘Excellency’ saboda za a iya kiran mutum kaɗai da ‘Excellency’ ne bayan ya kammala mulkinsa.

“A wannan lokacin ne mutane za su tabbatar na cancanci a kira ni da ‘Excellency’ ko kuma a’a”. Inji shi.

Zaɓaɓɓen gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Raɗɗa ya ci gaba da cewa, gwara al’uma su kira shi “Gwamna” ko kuma “Malam Dikko Raɗɗa” amma ba ‘yallaɓai ba har sai ya gama mulkinsa.

“A wannan lokacin mutane za su iya tabbatar wa na cancanci a yabe ni ko kuma a’a, ina tunanin zai fi kyau mutane su kira ni gwamna ko Malam Dikko Raɗɗa a kan su kira ni da ‘His Excellency’.

“Zan fi son haka saboda hakan ba zai fasa min kai ba”. Inji shi.

“Ina son in ji ni kamar kowa saboda haka, ba na son ‘Excellency’ ya shiga cikin kaina, wannan shine dalilin da ya sa ba na so a haɗa kalmar da sunana.” Inji shi.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC, ta ayyana ɗan takarar na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Katsina da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023.