Ku kiyayi kanku – Gargaɗin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Katsina ga ’yan bindiga

Daga UMAR GARBA a Katsina

Sabon Kwamishinan Rundunar ’Yan Sanda na  Jihar Katsina, CP Idris Dauda Dabban, ya gargaɗi ɓarayin daji, waɗanda suka addabi wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar ta Katsina, da su tuba ko kuma su fuskanci fushin rundunarsa.

CP Dauda ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar dake birnin Katsina a wani taron manema labarai na farko da ya gabatar bayan da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da shi a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar.

CP Dauda wanda ya gaji Sunusi Buba ya bayyana cewar babbar matsalar da rundunar ke fuskanta a jihar Katsina ita ce matsalar ‘yan bindiga dake yin sanadiyyar salwantar rayuka da dukiyoyin al’uma. 

“Dukkan mu mun san babbar matsalar da wannan rundunar ke fuskanta wadda galibinta ba ta wuce hare-haren ‘yan bindiga  don haka za mu haɗa kai domin ganin an kawo ƙarshen matsalar,” inji shi.

Ya kuma sha alwashin sai ya ga bayan dukkan wani ɗan ta’adda a ƙarƙashin jagorancinsa, daga nan sai kuma ya bayyana cewar zai ci gaba daga inda tsohon kwamishina CP Sunusi Buba ya tsaya. 

Ya ƙara da cewa zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jami’an tsaro dake jihar domin kakkaɓe masu aikata miyagun laifuka.

Daga ƙarshe CP Dauda ya roƙi al’ummar jihar Katsina musamman waɗanda ke zaune a yankin da ‘yan ta’adda su ka fi yin ta’addanci akan su ci gaba da bai wa rundunar haɗin kai domin samun nasara  sai kuma ya buƙaci jami’ansa akan su ƙara ƙaimi wajen yaƙar ‘yan ta’adda a jihar.

Kafin naɗin Idris Dauda Dabban a wannan matsayi shine babban jami’in sadarwa a ɓangaren yaɗa labarai da sadarwar kimiyyar zamani na rundunar ‘yan sanda dake Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *