Ku mara wa wanda zan kawo a zaɓen 2023 – El-Rufai ga ‘yan Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya yi kira ga jama’ar jihar da su yarda da shi su mara wa duk ɗan takarar da ya ɗaga wa hannu kakar zaɓen 2023, domin a cewar sa shi ya fi cancanta kuma ya san zai zama gwarzon gwamna.

Manhaja ta ruwaito yadda Malam Nasiru El-Rufai ke magana a cikin wani faifan bidiyo cikin harshen turanci yana cewa “wasu suna cewa wai abinda muka yi a yanzu ba za yiwu a maida hannun agogo baya ba, to ba haka ba ne, muddin aka yi rashin sa’a wani talasurun ɗan PDP ya zama gwamna a Jihar Kaduna zai iya maida hannun agogo baya cikin wata shida. Don haka kada ma ku yi kuskuren zaɓar PDP a 2023.”

Gwamnan ya ƙara da cewa, “muddin aka zaɓi PDP to an maida hannun agogo baya, kuma a cikin ƙanƙanin lokaci komai zai lalace kamar a shekarun baya.

“Sannan don Allah idan muka tsaida ɗan takara a APC kuma na aminta da shi to ku yarda da ni ku karɓe shi hannu bibbiyu ku zaɓe shi, domin wannan ɗan takarar na yi amanna jajurtacce ne wanda zai riƙe amanar Jihar Kaduna daga 2023 kuma zai yi aiki tuƙuru,” inji gwamnan.

Ko a kwanakin baya Gwamna Nasiru El-Rufai a wata hira da ya yi da gidan talabijin na ARISE TV ya hori al’ummar Jihar Kaduna da kada su kuskura su zaɓi jam’iyyar PDP a zaven 2023.