Ku sauke farashin fiya wata ko a saka muku takunkumi, Ƙaramar Hukumar Keffi ga kamfanoni

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Hon. Muhammad Baba Shehu, ya bada umarnin gaggawa kan a sauke farashin ruwan leda da aka fi sani da ‘Pure Water’ daga N20 zuwa N10 kamar yadda lamarin yake a baya.

Baba Shehu ya bada wannan umarni ne a lokacin da ya yi wata ganawar gaggawa tare da ‘yan kasuwa masu sarrafa fiya wata a yankin Ƙeffi a ofishinsa da ke sakatariyar ƙaramar hukumar a ranar Alhamis

A cewar Baba Shehu, ƙarin farashin ruwan da kashi ɗari da ‘yan kasuwar suka yi sun yi haka ne don amfanin kansu ba tare da la’akari da ɓangaren al’ummar da suke amfani da ruwan ba balle kuma tuntuɓar hukuma kafin ɗaukar matakin.

Don haka sbugaban ya kafa wani kwamiti na musamman da zai zauna ya yi wa lamarin kallon basira don samar da maslaha, tare da umurtar ‘yan kasuwar da su miƙa sunayen mutum uku daga cikinsu da za su zama mambobi a kwamitin.

Daga nan, Baba Shehu ya gargaɗi ‘yan kasuwar kan cewa idan suka kuskura suka ƙetare umurnin da ya shata musu, to, ko shakka babu za ƙaƙaba musu takunkumi a harkokin kasuwancinsu.

Tun farko da yake jawabi, sakataren ƙungiyar masu sarrafa fiya wata a yankin Keffi, pastor Daniel Okorie, ya ce tsadar kayan aiki ya haifar da tashin farashin fiya wata da ake fama da shi a halin yanzu.

Ya ƙara da cewa, ƙarin farashin ba wai ya taƙaita da ƙaramar hukumar Keffi ne kawai ba, amma cewa abu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya.

A halin da ake ciki, yanzu jakar fiya wata guda a garin Ƙeffi ana sayar da ita ne tsakanin N200 zuwa N250. Yayin da ake sayar da ledar fiya wata ɗaya tsakanin N15 zuwa N20.