Ku tsayar da ni takara ku ga yadda zan ci zaɓe cikin ruwan sanyi, Tambuwal ga PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato, ya roƙi jam’iyya ta duba yiwuwar tsayar da shi takara a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Tambuwal ya ce matuƙar PDP ta ba shi tikitin takara to zai share mata hawaye ya dawo mata karagar mulkin Nijeriya.

A cewar gwamnan, da zaran ya zama shugaban ƙasa zai ɗauko mambobin jam’iyya ya naɗa su manyan muƙamai.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban mai taimaka masa ta ɓangaren yaɗa labarai, Muhammad Bello, kuma aka raba wa manema labarai.

A cewar sanarwan, Tambuwal ya yi roƙon ne yayin ganawa da tsofaffin ‘yan majalisu a babban birnin tarayya Abuja, ranar Talata.

Gwamnan ya faɗakar da PDP ta canza tunani game da tsarin karɓa-karɓa, ka da ta ce dole sai ɗan wani yanki za ta tsayar takara, wanda wasu ke goyon bayan haka.

Ya kuma tuna wa jam’iyyarsa matakin da APC ta ɗauka na watsi da zancen yanki, suka kai takara jihar Katsina, inda Mariyayi Umaru Musa Yar’adua, ya fito.

“Za mu iya raba tikitin amma wajibi mu yi tsarin da za mu ci nasara, tilas PDP ta rungumi abin da ke zahiri,” inji Tambuwal.

Gwamnan na Sakkwato ya kuma bayyana hasashensa kan hanyoyin da jam’iyyar PDP za ta bi ta samu nasara a babban zaɓen shugaban ƙasa dake tafe a 2023.

Ya ce APC na da ƙarfi a Arewa da gwamnoni 16, haka PDP tana da ƙarfi a Kudu, don haka wajibi PDP, “ta yi tunani mai kyau, tsari mai kyau kuma ta lashe zaɓe.”