Ku yi amfani da finafinaku wurin haɓaka zaman lafiya da haɗin kai, Sanata Barau ga Kannywood

Daga AISHA ASAS

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya buqaci ‘yan wasan kwaikwayo a masana’antar nishadantarwa ta Kannywood da su yi amfani da finafinansu wajen tallafa wa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar nan.

Sanata Barau ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karvi bakuncin shugabannin ƙungiyar jaruman Kannywood a ofishinsa da ke harabar Majalisar Dokokin Ƙasa da ke Abuja.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ismail Mudashir ya fitar, Sanata Barau ya jaddada muhimmancin masana’antar wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar nan.

Idan har ana so gwamnati ta samu nasarar shawo kan ‘yan fashi da garkuwa da mutane da sauran ƙalubale, ya ce, dole ne masu ruwa da tsaki su goyi bayan wannan koƙarin, ciki har da na masana’antar nishaɗantarwa.

“A masana’antun finafinai za ka tarar da ayyukan yi ga mutane da dama waɗanda su ma za su ɗauki wasu. Wannan babban gudunmuwa ce ga cigaban ƙasa.

“Kuna da babbar rawa da ku ke takawa a wurin samar da zaman lafiya da haɗin kai. Don haka ku yi amfani da finafinaku wurin ba wa gwamnati goyon baya a ƙoƙarin da take yi na shawo kan matsalar tsaro da ta addabi Arewacin Nijeriya.

“Kuna da damar amfani da finafinanku wurin shawo kan ‘yan fashin daji da masu satar mutane da ke daji da su ajiye makamai, su tuba, kuma su canza rayuwar da suke yi. Wannan shi ya kamata mu ba wa muhinmanci a wannan lokaci.

“Kuma a cikin duk abinda za mu yi, mu tabbatar ba mu kauce wa koyarwar addininmu ba,” cewar Sanata Barau.

Yayin da yake jaddada ƙoƙarin majalisar dokoki kan cigaban harkar nishaɗantarwa da ke ƙasa, ya amince da zama uba ga kungiyar kamar yadda suka bukata, tare da alƙawarin ci gaba da ba su gudunmuwa.

Jaruman sun bayyana Sanata Barau a matsayin babban ginshiƙi, uba ga masana’antar Kannywood.

Da yake magana da yawun bakin jaruman, shugaban tafiyar Alhaji Alasan Kwalle, ya ce, “Kai wani givi ne gare mu, tsayin shekaru kana ba mu gudunmuwa. Muna matuƙar godiya ga irin abinda ka ke yi mana.”

Shi ma a nasa jawabin, shugaban kwamitin amintattu, Alhaji Shehu Hassan Kano, ya tabbatar wa sanatan za su haɗa kai da gwamnati wurin samar da zaman lafiya da haɗin kai a ƙasa bakiɗaya.