Daga UMAR GARBA a Katsina
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ba wa al’ummar Jihar Katsina haƙuri dangane da mawuyacin halin da ‘yan jihar da ma ƙasa baki ɗaya aka shiga sakamakon canjin kuɗi da Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya yi.
Buhari ya bayyana haka ne ran Laraba cikin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar a gidansa da ke Daura.
“Ina ƙara maku godiya da yarda da kuka yi da ni kuka zaɓe ni har sau biyu a matsayin shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.
“Ina baku haƙuri kan wahalar da aka sha ta canjin kuɗi an yi ne don haɓɓaka tattalin arziki”. Inji shi.
Haka zalika, Buhari ya roƙi al’ummar jihar da su fito ranar 11 ga watan Maris, 2023 don zaɓen ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC wato Dikko Umar Raɗɗa da kuma ‘yan majalisar jiha na jam’iyyar.
A cewar Buhari, ƙwarewar Raɗɗa za ta kawo wa jihar cigaba sosai.
Daga ƙarshe ya yi fatan samun zaman lafiya da kammala zaɓukan gwamnoni da ‘yan majalisar jiha lafiya.