Ku yi watsi da saƙonnin ƴan damfara – NELFUND ga ɗalibai

Daga BELLO A. BABAJI

Asusun bada Aron Kuɗin Karatu ga ɗalibai (NELFUND), ta gargaɗi ɗalibai da su guji cike bayanan neman aron kuɗaɗe daga shafukan bogi.

Cikin wata takarda da Daraktan yaɗa Labarai na NELFUND ya aika wa Blueprint a Abuja, ta yi kira ga ɗalibai da ɗaukacin al’umma da su yi watsi da duk wani shafi ko saƙo da ke ikirarin daga NELFUND ya ke.

Sanarwar ta jaddada cewa, halasttaccen shafin NELFUND ga ɗalibai guda ɗaya ne, kuma shine kamar haka; www.nelf.gov.ng.

Ta kuma ce, ta na cigaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa duk wani ɗan Nijeriya da ya cancanta, ya samu damar karɓar aron kuɗin karatu.

Kazalika, ta shawarci al’umma da su riƙa bibiyar sahihin shafin da ta amince da shi don samun bayanai masu amfanarwa.