Ku zamo jakadun ƙwarai a ƙasa Mai tsarki, kiran Gwamnan Zamfara ga maniyyan jihar

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi kira ga maniyyatan aikin hajjin bana na jihar da su zama jakadu nagari yayin da suke ƙasa mai tsarki.

Ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a yayin da yake bankwana da maniyyatan jihar su 428 da za su tashi a jirgin farko zuwa Saudiyya don sauke farali.

Gwamna Matawalle wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Sanata Hassan Nasiha, ya ce gwamnatinsa ta yi duk wani shiri na tabbatar da jin daɗi da walwalar alhazan jihar yayin da suke ƙasa mai tsarki.

“Muna kira ga maniyyatanmu da su kasance masu nagarta tare da addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya a jihar,” in ji Gwamnan.

A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar, Alhaji Lawal Isah Abdullahi, ya bayyana cewa adadin maniyyata 3,100 ne za su halarci aikin Hajjin bana kamar yadda Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta amince.

A cewarsa, tuni dukkan maniyyata 3,100 sun samu riga-kafi kafin su tafi ƙasar Saudiyya”.

Ya ci gaba da cewa, hukumar ta samar da matsuguni masu nagarta kuma kusa da Masallacin Harami don sauƙaƙa wa alhazan jihar ayyukan Hajji.

“Ya zuwa yanzu mun samu kashi 85% na biza ga maniyyatanmu, kuma mun gargaɗe su da su guji yin jigilar kayayyakin da aka haramta zuwa da su Saudiyya, saboda dokokinsu sun sha bamban da na ƙasarmu,” inji shi.