Ku zauna da shirin karɓar baƙuncin EFCC, shawarar Ɗankwambo ga gwamnoni masu barin gado

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya shawarci gwamnoni masu barin gado da su zauna da shirin karɓar baƙuncin hukumar EFCC da ICPC da dangoginsu waɗanda za su yi musu tambayoyi masu buƙatar amsoshi.

Ɗankwambo ya shawarci gwamnonin ne a wajen taron walimar ban-kwanan da da aka shirya musu a Otel ɗin Transcorp da ke Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.

Da yake jawabi a wajen taron, tsohon gwamnan Jihar Kwara, Bukola Saraki, ya yi kira ga gwamnoni 18 masu barin gado da su sai-saita kansu bayan barin mulki don cigaban ƙasa.

Saraki ya ce, “Bayan kun bar kujerar gwamnan, ku qyale magadanku su yi aikinsu. Ku koma ga iyalanku, na tabbata matanku, ‘ya’ya da jikokinku suna ƙidaya kwanakin da suka rage muku.

“Za ku shiga wata sabuwar rayuwa ce wadda take daban da inda kuka baro. Ku killace kuɗinku don sayen abinci da raguna don kuwa ba za ku same su kamar yadda kuka saba ba.”

A hannu guda, tsohon Shugaban Majalisar Dattawar ya yi kira ga gwamnoni masu jiran gado da su yi ingantaccen tsari kan yadda za su tafiyar da mulkinsu, sannan kuma su fara shirye-shiryen barin kujerar mulki daga ranar farko da suka kama mulki.