Ku zo mu haɗa hannu mu ceci Nijeriya, cewar PDP ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin shirya babban taron jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zo su haɗa hannu da jam’iyyarsu don karɓe mulkin ƙasa da kuma gyara wa ƙasar zama.

Fintiri ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabin maraba da dalaget da jami’an jam’iyya wajen babban taron PDP na 2021 ranar Asabar a Abuja.

Yana mai cewa, babban taron nasu shi ne mataki na farko na shirin ceto Nijeriya da jam’iyyarsu ta yi.

Ya ce, “Za mu karɓe ƙasarmu kamar yadda muka saba. Ya kamata mu ceto Nijeriya, tun da har muka iya raba sojoji da mulkin ƙasa, za mu iya tunkarar wannan gagarumin aikin.

“Za mu iya kawar da mutanen da ko ma’anar shugabanci mai nagarta ba su sani ba daga ƙaragar mulki.

“wannan shi ne ƙudurin ceto Nijeriya, kuma wannan shi ne rawar da aka assasa PDP don ta taka.

Gwamnan ya ce Nijeriya ta faɗa cikin wani hali wanda ya kai ga yanayin ƙasar babu daɗi. Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu Nijeriya ba ta amsa sunan nan na jarumar Afrika saboda halin da ta tsinci kanta ciki.

Fintiri ya faɗa wa dalaget cewa taron wata dama ce da ya kamata su yi amfani da ita wajen kama hanyar da ta dace game da makoma da kuma alƙiblar jam’iyya.

Ya ce baki ɗaya mutum 34 suka nuna sha’awar riƙe muƙamai daban-daban a jam’iyyar a matakin ƙasa, inda bayan tantancewa mutum 28 sun tsallake, biyu sun janye bisa ganin damarsu, sannan an samu mutum huɗu da rashin cancanta.

Ya ce gurbin muƙamai 21 ake da su, yayin da dalaget 3,600 ne aka shirya za su kaɗa ƙuri’a don zaɓen jami’an da za su ci gaba da jan ragamar harkokin jam’iyyar. Don haka ya yi kira ga waɗanda lamarin ya shafa da su yi zaɓen nasu da lura don cigaban jam’iyyar.