Kula da ƙafa da gashi a lokutan sanyi

Daga AISHA ASAS 

A satin da ya gabata, mun kawo yadda za ki iya kula da fatarki, da kuma ɗabi’un da ya kamata mu dinga yi a lokacin sanyi. A yau za mu taɓo wani ɓangare da ke buƙatar kulawa a lokacin sanyi, wato ƙafa da kuma gashi.

A lokacin sanyi ba iya fata ke shiga yanayi ba, asali ma ga wasu ƙafa ta fi shiga mawuyacin hali fiye da sauran fatar jiki.

Kafa wata muhimmiyar ɓangare ce a jikin mutum da ya kamata a ba ta kulawa ta musamman a lokacin sanyi. 

Ta yaya za a iya kula da ƙafa a lokacin sanyi?

Za ki iya amfani da hanya mai sauƙi wurin kula da ƙafa ta hanyar amfani da gishiri, ruwan kal (vinegar), da kuma ruwan zafi.

Za a samu roba, a zuba ruwan zafi daidai da yadda ƙafar za ta iya ɗauka, a zuba ruwan kal da kuma ɗan gishiri, sannan a saka ƙafar a ciki, har tsayin lokacin da ruwan za su huce, sannan a yi amfani da dutsin goge ƙafa a goge ƙafar har sai duk wata mataciyyar fata ta fita. Sai a samu mai kamar man kaɗe ko makamantan sa, a shafe ƙafar da shi. Kuma a tabbatar da ba a bar ta ba mai ba. Domin ɗaya daga cikin ababen da ke ƙara matsalar akwai bushewa, kuma mai zai iya magance ta.

Sannan yana da kyau mu kula da suturce ƙafar, ba wai kawai don jin sanyi ba, sai don ba wa ƙafar kariya. Kuma hanya ce da za a rage mata saurin bushewa bayan an shafa mata mai.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.