Kunyar Buhari ta hana ni kashe APC a Daura, cewar Fatuhu Muhammad, ɗa ga Shugaban Ƙasar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Sandamu, Daura, Mai Adua a Majalisar Wakilai ta Ƙasa Honorabul Fatuhu Muhammadu, ya yi barazanar ficewa daga Jam’iyyar APC matsawar ba a dawo masa da kujerarsa ba. 

Fatuhu Muhammad, wanda ya yi wannan barazanar a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a taron da ya kira a Daura, ya bayyana cewa duk jam’iyyar da ya kawo a mazaɓarsa ita ce za ta ci zaɓe. 

Kamar yadda jaridar Katsina Post ta nakalto, taron ya samu halartar jiga-jigan siyasa a jam’iyyar APC, da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin ƙananan Hhukumomi uku da yake wakilta.

Fatuhu Muhammad, wanda ɗa yake ga Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa kunyar Baban nasa ce ta hana shi kashe Jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Daura, sakamakon rashin adalci da aka nuna masa a lokacin gudanar da zaɓen fidda gwani na Ɗan Majalisa.

Ɗan majalisar Fatuhu Muhammdu ya ce abun baƙin ciki ne garin Shugaban Ƙasa a ce ba a gudanar da zaɓe ba, don kawai wasu mutane na ganin bai kamata a bai wa al’umma zaɓinsu ba.

“Na rantse da Allah mun bi duk matakin doka, bayan wasan yara, mai suna zaɓen fidda gwani, kuma muna nan muna jiran Jam’iyyar APC ta kasa mu ga wane mataki za ta ɗauka kafin watan Agusta da za a tura dukkanin sunayen ‘yan takarkaru,” inji Fatuhu.

Ya ƙara da cewa, a saboda haka, kuma a halin yanzu ya umarci duk wani magoya bayansa da kada ya mara wa ɗan takarar da aka ɗora na ƙananan hukumomin Daura, Sandamu, Daura, har sai an ga matakin da aka ɗauka.

A kan batun barin Jam’iyyar APC, Honorabul Fatuhu Muhammdu ya ce, “komai zai iya faruwa. Ma’ana zan iya barinta, siyasa ba addini ba ce. Don haka zan iya yin komai. Addini ne kawai mutum zai yi dole. 

A kan buƙatar sake gabatar da ƙudirin Jami’ar Sufuri ta Daura, ɗan majalisar ya ce zai yi duk abin da zai iya kafin nan da sati takwas, ko bayan majalisar ta dawo hutu, domin ganin jami’ar ta zama doka.

A jawabinsa a taron, Shugaban Ƙaramar Hukumar Daura, Alhaji Bala Musa Daura, ya bayyana jin daɗinsa na kulawar da ɗan majalisar ke nunawa ga al’ummarsa, musamman yadda ya kira taron sada zumunci.

Alhaji Bala Abdu Daura ya ce ana buƙatar shugabanni da nuna son talakawansu, da kuma nuna kulawa gare su. Sai ya yi addu’a ga Allah ya saka masa da alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *