Kushen rashin adalci kan Ma’aikatar Jinƙai ta Tarayya

Daga RA’AYIN BLUEPRINT

Farmakin da ake ta kai wa ma’aikatar jinƙai da kiyaye ibtila’i da tallafa wa al’umma ta Nijeriya a ‘yan kwanakin na a kan ambaliyar ruwa a fadin ƙasar nan babu adalci a cikinsa kuma ya sanya ma’aikatar a cikin tsaka mai wuya.  

Wato dai wannan ma’aikatar ta jinƙai a ƙarƙashin jagora Hajiya Sadiya Umar Farouq, mutane na tuhumarta ne da vangaranci na fifita yankin Arewa da yi musu alfarma iri-iri fiye da sauran yankuna.

A haƙiƙanin gaskiya dai da ma tun farko ambaliyar ruwan yankin Arewa ya fara tavawa kafin ya tsallaka zuwa Kudancin Nijeriya irin su Anambra, Dalta, Ribas, Bayelsa da sauransu. 

Sakamakon rahotannin bincike dai sun tabbatar da cewa, ambaliyar ta taɓa wasu ɓangarori na dukkan jihohi Nijeriya 36 har ma da Abuja.

Hakazalika, rahotannin sun bayyana cewa, mutane 612 ne suka rasu a sakamakon ambaliyar, mutane 3,219,780 kuma suka cutu a dalilinsa, sannan mutane 1,427,370 suka rasa matsugunnansu, sannan mutane 2,776 su suka jikkata a sanadiyyar ambaliyar. 

Bugu da ƙari, mutane 181,600 su ma gidajensu sun ɗan rushe, mutane kuma 123,807 gidajensu sun rushe bakiɗaya, haka gonaki masu girman kadada 176,852 su ma sun daan taɓu yayin da kadada 392,300 na gonakin sun shafe gabaɗaya.  

Wataqila dalilin da ya sa ake tsammanin ma’aikatar jin ƙan ta ɗauki nauyin dukkan waɗannan matsalolin shi ne, saboda ana ganin shi ne mafi munin ambaliyar da aka taɓa yi a tarihi.

Wato bayan wanda ya afku a shekarar 2012. Shi ya sa wasu mutanen ba sa tunanin sauran ma’aikatun gwamnatin da su ma wannan nauyin ya hau kansu. Ba hukumar kaɗai ba ce. 

Haka akwai kuma hukumomin da ma suna aiki ne da Umarnin hukumar kuma suna amsa kiran da aka yi musu don kawo ɗauki a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. 

A taƙaice, bayan ma’aikatar jin-ƙai akwai ma’aikatun, muhalli, albarkatun ruwa, noma da kiwo, aiki da gidaje, hukumar ba da ɗaukin gaggawa su ma suna da alhakin gyara Nijeriya da kawo ɗauki a duk lokacin da aka nemi ɗaukinsu. 

Sannan akwai hukumar cigaban Neja Delta (NDDC) wacce take da alhakin kula da dukkan sassa  Kudu maso kudancin ƙasar nan da suka haɗu da matsalar ibtilai.

Kamata yadda ita ma NDDC ta yi koyi da takwararta Hukumar cigaban Arewa maso gabacin Nijeriya  (NEDC), wacce take kawo ɗauki nan-da-nan da zarar wani ibtila’in ya samu jihohin da suke ƙarƙashinta.  

Sannan kuma duk da lalalcin da NDDC ta yi, hukumar ba da taimakon gaggawa ta NEMA wacce wani ɓangare ce ta Ma’aikatar ba da taimakon gaggawar ta ba da tallafi tare da taimakon Ma’aikatar jiragen sama ta Nijeriya. Inda aka raba kayayyakin rage raɗaɗi ga mutanen da ibtilain ya shafa a Kudu maso Kudancin. 

Abubuwan da aka rarraba sun haɗa da Buhunhuna 400  na shinkafa mai nauyin giram 10 buhunhuna 400 na masara mai nauyin giram, buhunhuna 300 na garin kwaki  mai nauyin giram 10, galan 50 na man gyaɗa, sai kayan 200 na tumatirin gwangwani, katan 200 na Indomi, bandir 200 na kwanon rufi, buhun sumunti, buhun ƙusa 40, da kuma fakitin ƙusar rufin kwano ma 200 da sauransu da suka haɗa da gidajen sauro, katan-katan na sabulai, shaddoji, kayan sawa, tabarmi da sauransu. 

Haka zalika, Hukumar NEMA ma ta ba da kayan rage raɗaɗi masu yawan gaske ga jihohin. Sannan kuma hukumar ta NEMA ta haɗa kai da Rundunar sojin ruwan Nijeriya (NNS) na Bayelsa da sauran masu taimakon sa kai wajen taimaka wa wajen kwaso mutane zuwa tudun tsira.

Abin takaicin shi ne, haka za mu yi ta koyon darasi mai wuya a kan ambaliya kowacce shekara. Saboda ko a bana tun watan Fabrairu hukumar qididdigar yanayi (NIMET) da hukumar NIHSA suka ba da hasashen hakan za ta faru.

Da wuraren da suke da haɗarin faruwar ambaliyar, inda a taronta na shekara mai taken AFO ya bayyana samun ambaliyar gabar kogunan a yankunan Ribas, Delta, Legas da jihar Bayelsa sannan za a yi a yi ambaliya a birane kamar Legas, Abeokuta, Osogbo, Ibadan, Benin, Asaba, Warri, Onitsha, Fatakwal, Kaduna, Sokoto, Yola, Abakaliki, Birni-Kebbi, Makurxi da sauransu a sakamakon rashin magudanan ruwa masu kyau. 

Sannan a ɓangaren shirya wa fatarar abinci a shekarar, NEMA ta shirya taron masu ruwa da tsaki a tsakanin 26 zuwa 27, ga watan Afrilun 2022 domin a tattauna matsalar ƙarancin abinci da ka iya faruwa.

A ƙarshen ganawar ta kwana biyu, masana suka yi gargaɗin kiyaye afkuwar ibtila’in ambaliya saboda zai iya shafar tattalin arziki da walwalar al’umma. 

Wannan hasashen masana da gargaɗin an aike da shi daga dukkan gwamnatocin jihohi Nijeriya guda 36 da Abuja. Domin su shirya wa tanadin da za su yi don kare dukiyoyin al’umma da rayukansu da lafiyarsu da matsugunnansu. 

Hakazalika NEMA ta rarraba taswirar NIHSA wacce take nuna dukkan yankunan da suke cikin haɗari. Tsahon  wannan lokaci hukumar ta NEMA ta yi aiki gaba da gaba da aiki tare da wayar da kan gwamnonin Nijeriya a kan su sauke nauyin da yake kawunansu na al’ummar jihohinsu su ɗauki matakai da tanade-tanade don kula da wannan gargaɗi da aka yi musu. 

Bayan haka kuma, hukumar ta shirya tarurruka bita a cikin watan Agusta waɗanda suka fi mayar da hankali a kan kauce wa Bala’ai don tanadi a kan hasashen da NIMET da NIHSA suka yi don shirya wa tare da tanadin magancewa da kiyaye afkuwar ambaliya a faɗin ƙasar. 

Sannan kuma hukumar ta samar da waƙoƙi da saƙonnin murya da ake sa wa a wasu zaɓaɓɓun gidajen yaɗa labarai da na rediyo na Turanci da harsunan gargajiya don gargaɗi a kan ambaliyar da kuma kiran a shirya yadda za a magance ta. 

Ba za a manta da irin gudunmowar da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar ba, na tan 12,000 na hatsi don rabawa a dukkan jihohi Nijeriya.  

Haka kwamitin ba da tallafi ga waɗanda ambaliya ta samu a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Aliko Dangote ta ba da kayayyakin abinci wanda darajarsu ta kai Naira biliyan 1.5 ga to NEMA wanda aka rarraba wa mutanen da abin ya shafa. 

A halin yanzu ma ma’aikatar tana tsara neman wa ƙasar tallafi daga bankin Duniya don tallafa wa waɗanda ambaliyar ta rutsa kamar yadda suka tallafa a shekarar 2012.

Don haka, ma’aikatar jinƙai ta cancanci yabawa saboda irin ƙoƙarinta na kawo ɗauki ba wai kashewa take buƙata ba. Dukkan hukumomi da jihohi ya kamata su haɗa kai da ma’aikatar don sauke nauye-nauyen al’umma na ceto su daga halin da suke ciki.