Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Ƙungiyar masu hada-hadar sayar da wayar salula a Jihar Kano da aka fi sani da AMPAT ta koka akan matakin ɗaukar doka a hannu da al’ummar Kano suka soma ɗauka na ƙone babura masu ƙafa uku da ake zargin na masu ƙwacen waya ne da cewa kuskure ne.
Kakakin ƙungiyar na AMPAT, Alhaji Ashiru Yusuf Yakasai ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da ya yi da manema labarai.
Ya ce ɗaukar irin wannan matakin bai kamata ba saboda za ta iya shafar wanda ba ruwansa.
Ashiru Yusuf ya yi nuni da cewa abinda ya kamata mutane subyi shine su daɗa ƙaimi wajen matsantawa ‘yan majalisar dokokin jihar Kano akan su zartar da doka mai tsanani akan duk wanda aka kama ya zare makami ya yi ƙwacen waya.
Kakakin na ƙungiyar AMPAT ya yi kira ga al’umma akan su kula da tarbiyya da ilimin ‘ya’yansu da kuma ɗora su akan yin ƙananan sana’oi da hakan zai taimaka sosai wajen kandakar ki wajen jefa matasa cikin munanan ayyuka.
Ashiru Yusuf Yakasai ya yaba wa jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda ƙarƙashin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Muhammad Husain Gumel bisa ƙoƙarin rundunar wajen ganin an daƙile harkar fashin waya a jihar.