Kutumbawa su ne tushen arzikin Kano – Farfesa Abdallah

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce Kutunbawa su ne tushen arzikin Kano, saboda sai da suka shuka suka kafa sannan wasu suka zo suka girba, idan da ba su yi ba babu wanda zai yi.

Farfesa Abdallah ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na zuriyar Kutunbawa da ya gudana a Rumfa College da ke Kano.

Farfesan ya ci gaba da cewa idan da ba su yi ba babu wanda zai yi, idan da sun lalatar da abin da ba za ka ji a na yi wa Kano kirari da Ko da me ka zo an fika ba, amma tun lokacin Abagayawa Kano ta ke da wannan arzikin.

“Kutunbawa da Fulani duk ɗaya ne kada mu yadda a kawo mana rabe-rabe ko wata fitina, abinda zai ɗaukaka a wajen Ubangiji ba imaninka ba ne ba Fulatancinka ba ne imaninka, domin shi ya kamata ya zame maka jagora domin haka babu abinda zai hana mu haɓaka al’adunmu,” inji Farfesa Abdallah.

Sannan ya bada shawarar ga Kutunbawa da a samu ranar haihuwar Alwali za a riqa tunawa da ita duk shekara sai a riqa yin bukukuwa sai ta zama ranar Alwaliy.

A ta’aliƙinsa Malami a tsangayar tarihi na Jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Tijjani Muhammad Naniya ya ce sarakunan Kutumbawa su ne suka bada gudunmawa Bahaushe ya zama abinda ya zama dole mu girma su mu yi masu addu’a.

“Domin da ba don gudummawar da suka bayar ba; to da ina Kanon take? Kano ai ta samu ne domin ƙoƙarin da suka yi da ba su yi ba ina Kanon ta ke? Ya bada amsa da cewa ba kowa, ai ba ma za a zauna ba saboda duk wanda ya zauna za a zo a yaƙe shi, su ke suka zauna suka bai wa Kano asali suka bai wa Kano mazauni suka bai wa Kano tsaro wannan Badala da ta kewaye Kano wanda a yanzu ake rusa mana ita asali da daraja da bunƙasar Kano,” inji Farfesa Naniya.

Shi ma da yake nasa jawabin Mai Unguwar Kutunbawa Kano Alhaji Mustapha Abubakar ya ce shekara 10 ana wannan taro amma bai ba a yin irin wanda ya kayarar ba irin na wannan shekarar.

Sannan ya gode wa farfesoshi da Sarakuna da ‘yan jarida da dukkanin ‘yan wannan zuriya mata da maza da suka halarci taron.