Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Keffi ta rantsar da sabbin ɗalibai 624

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Sama da ɗalibai 624  ne suka ɗauki rantsuwar kasancewa ɗaliban Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta gwamnatin jihar Nasarawa dake garin Keffi, wato College of Health, Science and Technology nagari a lokacin wani babban bikin ɗaukar rantsuwa da kuma yaye wasu ɗaliban kwalejin wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na sabon ginin kwalejin da ke kan hanyar Keffi zuwa Abuja a ƙarshen makon da ya gabata. 

A jawabin shugaban kwalejin Alhaji Suleiman Abdullahi Mohammed ya faro ne da bayyana tarihin kwalejin a taƙaice, inda ya ce an kafa shi ne a shekarar 1999 da nufin samar da ingantaccen ilimin kiwon lafiya don kula da lafiyar al’umma baki ɗaya kuma a cewarsa kawo yanzu kwalejin tana cimma burin sakamakon yaye ɗalibai da ke bada gagarumar gudunmawa a fannin kiwon lafiyar a jihar da ƙasa baki ɗaya. 

Bayan ya taya sabbin ɗaliban murnar nasara da suka samu na fara karatu a kwalejin, ya bayyana cewa daga cikin sama da ɗaliban 1000 da suka nemi gurbin karatu a kwalejin sune kaɗai suka yi nasara, saboda haka a cewarsa bai kamata su yi wasa da wannan dama da suka samu ba. 

Ya kuma gargaɗi sabbin ɗaliban na zangon karatun shekarar 2021 da 2022 su tabbatar sun guje wa duk wata ɗabi’a da ka iya hana ruwa gudu a kwalejin kasancewar a cewarsa kwalejin ba zanta ƙyale duk ɗalibi ko ɗaliba da aka kama da laifin ba. 

Alhaji Suleiman Abdullahi Mohammed ya kuma ja hankulan sabbin ɗaliban musamman dangane da shiga ƙungiyoyin asiri a ciki da wajen kwalejin, inda ya shawarce su cewa su riƙa kula da harkokin karatunsu a yayin zaman su a kwalejin kaɗai. 

Ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar cewa nan ba da daɗewa ba kwalejin za ta fara gudanar da wasu kwasa-kwasan digiri don amfanar ɗalibai da dama da ke son ci gaba da karatunsu a kwalejin da sauransu. 

Sauran abubuwa da aka gudanar a yayin taron ɗaukar rantsuwar sun haxa da ɗaukar rantsuwar kasancesa ɗaliban kwalejin nagari da sabbin ɗaliban suka yi da yaye wasu ɗaliban da suka kammala karatun su a kwalejin, inda aka rarraba musu satifiket ɗin kammala karatun da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *