Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Keffi ta yi bikin yaye ɗalibai

Daga BASHIR ISAH

Kwalejin Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Jihar Nasarawa da ke Keffi, ta yi bikin yaye ɗalibai da suka kammala difloma a fannin kimiyyar abinci (Nutrition and Dietetics).

Bikin yayewar ya gudana ne a ranar Larabar da ta gabata a babban zauren taron kwalejin a sabon gininta da ke yankin Sabon Gari cikin ƙaramar hukumar Keffi, inda aka yaye tare da rantsar da ɗalibai su sama da sittin a matsayin cikakkun mabobin Ƙungiyar Masana Kimiyyar Abinci ta Nijeriya (IDN).

Tun farko a jawabinsa na maraba, shugaban kwalejin, Suleiman A. Muhammad ya ce wannan shi ne karon farko da makarantar ta shirya bikin yaye ɗalibai makamancin wannan. Tare da cewa, wannan su ne rukuni na shida na ɗaliban da suka kammala kwas ɗin nazarin kimiyyar abinci a kwalejin, kwas ɗin da aka ƙaddamar da shi a kwalejin a 2012.

A cewarsa, kawo yanzu kwalejin ta yaye ɗalibai 568 a wannan fannin a tsakanin 2015 da 2021.

Suleiman ya zayyano wasu nasarori da suka haɗa da ƙulla ƙawance da wasu jami’o’i don yin aiki tare, bunƙasar ƙoƙarin ɗalibai, samun goyon bayan gwamnatin jihar wajen biyan buƙatunta da dai sauransu.

Daga nan, ya yi kira ga ɗaliban da aka yayen da su zamo jakadu nagari a duk inda suka tsinci kansu, kana ya yi musu fatan alheri.

Da take bayani a wajen taron, shugabar taro kuma babbar hadima ga Gwamnan Jihar Nasarawa kan sha’anin kula da lafiya a matakin farko, Princess Elayo, ta nusar da ɗaliban muhimman damar da suke da ita a matsayinsu na waɗanda suka nazarci kimiyyar abinci. Tare kira a gare su da maida hankali wajen yin abin da zai amfani rayuwarsu da ma jiha baki ɗaya da ilimin da suka damu.

Taron ya shaida shan ratsuwar zama mambobin IDN da ɗaliban suka yi ƙarƙashin jagorancin jami’an IDN na ƙasa, an kuma miƙa wa kowannensu shahadar kammala karatu.

Taron wanda ke da harshen damo, wato bikin yaye ɗalibai da kuma babban taron IDN na ƙasa, ya samu mahalarta daga sassan ƙasar nan.