Kwamishina Waiya ya buƙaci gidajen jaridu su cigaba da nuna ƙwarewa a ayyukansu

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamishinan yaɗa Labarai da Harkokin Cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga gidajen jaridu da su cigaba da kiyaye ƙwarewa a harkar jarida.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin wata tawagar masu kishin al’umma a ofishinsa.

Ya jaddada cewa, ma’aikatarsa ta na cigaba da ƙoƙarin haɗa hannu da Hukumar Watsa labarai ta Ƙasa, NBC, don wayar da kan gidajen jaridu wajen inganta abubuwan da suke yaɗawa.

A wata sanarwa da Daraktan Ayyuka na Musamman na Ma’aikatar ya fitar a ranar Litinin, Waiya ya nuna buƙatar wayar da kan masu tsokaci akan harkokin siyasa musamman waɗanda ake kira da sojojin baka a yayin da suke bada gudunmawa a shirye-shiryen siyasa na gidajen rediyo.

Ya kuma yi kira ga jagororin Kano da mazauna manyan biranen Nijeriya kamar su Abuja, Legas da Fatakwal da su bada gudunmawarsu ga ci-gaban jihar.

A nasa jawabin Shugaban tawagar, Abdurrahman Baffa Yola, wanda tsohon mai bai wa Shugaban ƙasa shawara ne kan harkokin siyasa, ya taya Kwamared Waiya murnar samun muƙaminsa na kwamishina, ya na mai jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar bisa naɗa shi da ya yi saboda cancantarsa.

Ya nuna damuwa kan yadda kalaman wasu ƴan siyasa kan iya haifar da tarzoma ko cin mutuncin waɗanda ake girmamawa, ya na mai nuna muhimmancin tabbatar da ƙwarewa a yayin gudanar da shirye-shiryen gidajen jaridu.