Kwamishinan ƙananan hukumomin Kano ya nemi taimakon NULGE

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Harkokin Ƙananan Hukumomi na Kano, Alhaji Muhammad Tajuddeen Othaman Zaura ya buƙaci ma’aikata a ƙananan hukumomin jihar da su taimaka wajen cimma nasarorin ci-gaba a jihar.

Kwamishinan ya yi kiran ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin tawagar jagororin ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomin Nijeriya, NULGE, a ofishinsa inda ya bayyana su a matsayin ginshiƙin ƙaddamar da ayyukan bunƙasa ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Ya bayyana muhimman ayyukan biliyoyin kuɗaɗe da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar, waɗanda suka haɗa da gina titina, magudanan ruwa da kuma gina asibitoci da gyara wasu da sauransu.

Alhaji Zaura ya ƙara da cewa an naɗa kwamitin kula da ayyuka don tabbatar da yin su yadda aka tsara su da kuma tsare gaskiya da adalci ga al’umma.

Ya yi alƙawarin tafiya tare da mambobin NULGE wajen muhimman ayyuka da samar musu da hanyoyin karin kuɗaɗen shiga da kuma inganta ba su kulawa.

A nasa jawabin, Shugaban NULGE reshen jihar, Kwamared Muhammad Ibrahim ya ce sun ziyarci kwamishinan ne don taya shi murnar sauya masa ma’aikata da gwamnatin jihar ta yi da kuma gabatar masa da sababbin jagororin ƙungiyar.

Ya kuma tabbatar da cewa za su bada gudunmawar da kwamishinan ya buƙata gami da wayar da kan ma’aikata wajen kiyaye ayyukansu, kamar yadda jami’in yaɗa labaran ma’aikatar, Ɗahiru Lawan Ƙofar Wambai ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.