Kwamishinan Ganduje ya ajiye aiki duk da ƙin amincewa da murabus ɗinsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ranar Laraba da ta gabata ne dai kwamishinan kasafin kuɗi da tsare-tsare na jihar Kano, Alhaji Nura Dankadai ya miƙa al’amuran gudanarwar ma’aikatarsa duk da rashin amincewar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi na murabus ɗinsa.

Rahotanni sun nuna cewa a ƙarshen makon da ya gabata ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya ba da wa’adi ga masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara a zaven baɗi da su yi murabus kafin ko kuma ranar Litinin 18 ga Afrilu, kamar yadda dokar zaɓe, ta bana da aka yi wa kwaskwarima ta tanada.

To sai dai kuma kwamishinan, Nura Dankadai, wanda ya nuna sha’awar tsayawa takarar majalisar tarayya a mazabar Tudun-Wada an ce bai ji daɗin umarnin da aka ba shi na ya ci gaba da zama ba saboda jam’iyyar ta fi karkata wajen ba da tikitin takara a mazabar shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhassan Ado Doguwa zai koma majalisar tarayya.

An ce ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata kuma yana cikin kwamishinoni 3 da Ganduje bai amince da murabus ɗin nasu ba kamar yadda ya yi da Manajan Daraktan Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), Baffa Babba Ɗanan’agundi.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Manhaja cewa Dankadai, ya miƙa aiki ga babban sakataren ma’aikatar, Malam Auwalu Sanda kuma ya bar ma’aikatar ba tare da jin daɗi ba.