Kwamishinan Labarai na Kano ya je ta’aziyyar rasuwar Haruna Ɗanzago

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Amadu Haruna Ɗanzago biyo bayan rasuwar shahararren ɗan siyaysar kuma ɗan kasuwa.

A yayin ziyarar a daren Asabar, Waiya ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga al’ummar Kano da harkar kasuwanci da kuma ƙasa baki ɗaya.

Ya ce, rashin ya haifar da babban giɓi ga siyasa da kasuwanci, sakamakon muhimmiyar rawar da ya taka a ɓangarorin biyu.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su yi koyi kyawawan halayensa na shugabanci.

Kafin rasuwarsa, Ɗanzago ya riƙe muƙamin Daraktan Hukumar Kula da Shara da Tsaftace Muhalli ta jihar Kano (REMASAB).

Ya ƙara da cewa, za a cigaba da tunawa da attajirin bisa gudunmawarsa ga harkar tattali da siyasa ganin yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina al’umma musamman matasa.

Hallau, ya miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar da jagoran jami’yyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya na mai addu’a ga mamacin da fatan samun haƙurin juriya ga iyalansa.