Kwamishinan ‘Yan sandan Kano ya musanta zargin su na ƙin biyayya ga gwamnatin Jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kano, Ussaini Gumel ya ce bai taɓa ƙin girmama gwamnatin Jihar ba, biyo bayan kalaman Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’ar Jihar, Haruna Dederi a kansu na cewa suna ƙoƙarin yin tawaye gami da bijirewa shugabancin gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf.

A ranar Asabar da ta gabata ne, Dederi ya yi magana a kan hukumar inda ya bada misali da sanar da dakatar da bukukuwan sallah da ta yi ba tare da umurni ko sanar da gwamnatin Jihar ba wanda hakan ya sa suka nuna rashin jin daɗinsu ga hukuncin.

Kwamishinan, ya musanta zargin inda ya ce basu taɓa ƙin girmama gwamna Abba Kabir Yusuf ba, yana mai cewa abun mamaki ne ace hukumarsu na karɓar umurni daga wasu mutane da basu cancanta ba.

Gumel ya ƙara da cewa ce sun ɗauki matakin dakatar da bukukuwan sallar ne la’akari da rikicin Masarautar Jihar wanda kin yin hakan kan iya kawo barazana ga zaman lafiyar Jihar da al’ummarta baki ɗaya.