Kwamishinan ‘Yan Sandan Kebbi ya ɗabbaƙa gasar Alƙur’ani tsakanin jami’an ‘yan sanda

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ya ɗabbaƙa gasar Alƙur’ani tsakanin jami’an ‘yan sanda a jihar, inda mahalarta gasar karatun Alƙur’ani goma sha takwas ne daga sassa daba -daban na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi suka shiga gasar karatun Alƙur’ani da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi Alhaji Magaji Kontagora ya ɗabbaƙa.

Da ya ke jawabi yayin buɗe gasar karatun, Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Kebbi ya ce dalilin shirya wannan gasar tare da ɗaukar nauyin ta shi ne akwai buƙatar ‘yan sanda su ƙara samun kusanci da mahaliccinsu domin samun tsira ranar lahira.

Haka zalika akwai samun kusanci da Allah idan ana yawaita tilawar Alƙur’ani wanda yana haifar da tsoron Allah Maɗaukaki a zukatan mai karanta shi, musamman jami’an ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukansu.

Karatun Alƙur’ani yana kuma haifar da tsoron Allah da saka tausayi da ƙwarin gwiwa wajen ayyuka musamman a wajen ‘yan sanda da alhakin kare rayuwar al’umma da dukiyoyinsu.

Ya kuma yi kira da a matsayin su na ‘yan sanda Musulmi da su kasance jakadun Musulunci a duk inda suka samu kawunansu ba sai ga Musulmi ba kaɗai.

A yayin qaddamar da shirin a hedikwatar rundunar da ke Birnin Kebbi, Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu-Bashar ya yaba wa waɗanda suka shirya shirin bisa gagarumin ƙoƙarin.

Sarkin wanda ya samu wakilcin babban limamin masallacin tsakiya na Birnin Kebbi, Sheikh Muktar Abdullahi, ya buqaci jami’an tsaro da su kasance masu tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu.

A cikin karatunsa mai taken: “Muhimmancin karatun Alƙur’ani Maigirma da aiki da shi”, Sheikh Muhammad Rabi’u-Danjuma, ya ce Alƙur’ani zai tsaya ne ga mutumin da a ko da yaushe ya ke karanta shi a gaban Allah Maɗaukakin Sarki a ranar ƙiyama a matsayin lauyansa don bayar da shaida akansa.

Rabi’u Ɗanjuma Sani (Tafawa Ɓalewa) ya ce, Allah ya ɗora wa iyaye nauyin tarbiyyar ‘ya’yansu, wanda karatun Alƙur’ani yana ciki kuma zai sanya mutum samun girmamawa ta musamman daga wajen Allah ranar ƙiyama.

Wannan dai shine karo na farko da kwamishinan ‘yan sanda ya ƙirƙiro irin wannan a cikin rundunar ‘yan sandan ta jihar Kebbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *