Kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya ya bai wa al’ummar ƙasar Sin kofin Olympic

Daga CRI HAUSA

A wajen cikakken zama na 139 da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa wato IOC ya shirya a jiya Asabar a Beijing, shugaban kwamitin Thomas Bach, ya karrama al’ummar ƙasar Sin da kofin Olympics, da nufin gode musu saboda goyon-bayansu ga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na bana.

Bach ya ce, ba don goyon-bayan mutanen Sin ba, da ba za a iya shirya gasar bana tare da samun cikakkiyar nasara ba. Duk da cewa an shirya gasar bana cikin wani yanayi na kulle don hana yaɗuwar cutar COVID-19, amma Bach ya ji dadin cikakken goyon-baya daga al’ummar ƙasar Sin.

A wani labari na daban kuma, a jiya Asabar, Thomas Bach ya aike da saƙo zuwa ga shugaban CMG Mista Shen Haixiong, wato shugaban babban rukunin gidan rediyo da talabijin na ƙasar Sin, inda ya sake taya kafar CMG murnar samun nasarar gabatar da shirye-shiryen gasar Olympics ta bana, inda ya jaddada cewa, alƙaluman sun shaida cewa akwai ɗimbin mutanen da suka kalli gasar ta bana, al’amarin da ya nuna cewa mutanen ƙasar Sin suna ƙara nuna sha’awa ga wasannin motsa jiki na lokacin sanyi, kuma yana da yaƙinin cewa ruhin wasan zai ci gaba da zama a zukatan mutanen ƙasar.

Fassarawa: Murtala Zhang