Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An sake samun cunkoson ababen hawa akan hanyar Keffi zuwa Abuja a ranar Alhamis daidai Karu a Babban Birnin Tarayya Abuja a kusa da wurin da wata tanka ta fashe a ranar Laraba. Wannan kuma wata babbar tankar mota ce ta faɗi a kusa da gadar Karu da ke Abuja.
Motar dai kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna, ta faɗo ne a wani ɓangare na titin, lamarin da ya hana zirga-zirgar ababen hawa zuwa Nyanya.
Wani shaidan gani da ido ya shaida wa Blueprint Manhaja cewa tuni jami’an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da sauran jami’an tsaro suka fara aikin share fage domin dawo da zaman lafiya a hanyar.
Mazauna garuruwan Karu, Nyanya, Jikwoyi, Kurudu da ke cikin babban birnin tarayya, sai kuma Mararaba mai makwabtaka da Abuja da ke cikin jihar Nasarawa, a kodayaushe suna fuskantar cunkoson ababen hawa saboda zirga-zirgar ababen hawa a yankin.