Kwana ɗaya kafin bada rahoton hauhawar farashi, har yanzu shafin Hukumar Ƙididdiga a rufe yake

Daga BELLO A. BABAJI

A halin yanzu al’ummar Nijeriya suna jiran tsammanin samun rahoton hauhawar farashi yayin da ya rage kwana ɗaya Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar da shi, inda har yanzu shafinta na yanar gizo ya ke a rufe.

Sakamakon rahoton zai bada damar yanke hukunci game da tsarin sarrafa kuɗaɗe da kewayawarsu acikin al’umma.

Wa’adin fitar da bayanai game da matakin farashi na watan Disamba zai ƙare ne a ranar 15 ga watan Janairu.

Mutane da dama suna ganin akwai yiwuwar NBS ta rasa damar fitar da rahoton kamar yadda ta saba game da batutuwa masu muhimmanci da suka shafi harkar tattali.

A satin da ya gabata ne Shugaban ɓangaren ƙididdige farashi na NBS, Ayo Andrew ya ce za a fitar da rahoton a wannan watan na Junairu, kamar yadda ya bayyana a wani taron ƙara wa juna sani game da harkokin kasuwanci da farashi.

Masana harkar tattali sun yi hasashen samuwar saukar farashi a Nijeriya la’akari da yadda harkokin tattali ya ke gudana a ƙasar.