Kwana goman ƙarshe na Ramadan

Daga MARYAM BATOOL

Kwanaki goman ƙarshe na wannan wata mai albarka na Ramadan sun kasance wasu muhimmai kuma gwalagwalan ranaku ga dukkan Musulmi. Watan Ramadan wata ne da aka saukar da Alƙur’ani ga Manzon Allah (SAW), wanda ya zamo haske, madogara, garkuwa, arziki da kuma jagora ga musulmai. Manzon Allah (S.A.W) yana cewa; “Duk wanda watan Ramadan ya zo ya wuce ba a gafarta masa zunubansa ba ya zama babban asararre.”

A wannan wata ƙofofin aljannah a bude suke sannan an rufe na wuta. Don haka Musulmai suke zage damtse wajen samun rabon wannan watan. An ɗaure sheɗanu, kuma an buɗe ƙofofin rahama da gafara ga al’ummar Musulmai da muminai.

Sai dai kuma da yawan mu matasa ba mu damu da irin albarkar da take cikin wannan kwanaki na ƙarshe ba, za mu yi sallarmu ne fisha mu gama, kamar yadda muke yi a koyaushe, mu tashi mu yi tafiyarmu. Haka ma idan lokacin buɗe-baki ya yi, sai ya zama gabadaya ta abinci ake ba ta albarkar azumin da mukayi ba. Sai kawai a durfafa cin abinci ba tare da addu’a ba, sannan kuma ga tsananin mita akan azumin da muke. Yau azumi ya yi wahala, wasu su na azumin ma, amma burinsu kawai su kushe azumin, wanda gabadaya ba shi da kyau, kuma ba shi da amfani.

Haka sai wannan wata mai albarka ya zo ya tafi ba a tsinana komai ba, ana yau za a yi, gobe za a canja har dai ya zama kuma an zo goman ƙarshe. Anan wasu masu ragowar hankalin su kan nutsu su yiwa kansu faɗa su fara gyarawa, wasu kam haka zai zo ya tafi ba su waiwayo ba. Allah ya raba mu da asara, Ameen.

Babban abun da ya ke ɗauke mana hankali shi ne wayarmu, maimakon ta zama ita ce za ta tallafa mana wajen tsare-tsaren ibadarmu, sai ya zama ita ce ta ke ɗauke mana hankali. Daga wannan kafar soshiyal midiyar sai wannan. Daren da yakamata mu raba muna ibada sai ya zama shine muke kalle-kalle da jin kaɗe-kaɗe da hira a lokacinsa. Mu da ba mu tara uwar komai ba a duniyar, maimakon mu riƙe wannan damar ta amfane mu sai ya zama mu muke wasa da ita.

Manzon Allah (SAW), wanda aka yi duniyar da aljanna domin shi, yana tashi, shi da iyalinsa a daren wannan watan, domin samun albarkarsa, to ina kuma ga mu?

Akwai kuma waɗanda har ga Allah suna so suyi ibadar, amma kuma wani sanyin jiki da kuma ganin cewa ai kwanakin suna da yawa shi yake sa suke rasa wannan falala. Saboda sanin kanmu ne wannan Watan da ya shigo yake ƙarewa, domin kuwa ba na asararru bane.

Sai kuma wanda su ba azumin ne a ran su ba, su kawai Sallah suke jira. Sai watan ya shigo ya ƙare tanadin su da tunaninsu gabadaya yana kan kayan da za su saka da sallah, shagalulluka da dai sauransu. Babu laifi dan an yi ɗoki kuma anyi wa Sallah tanadi amma abin da ya fi dacewa shi ne a fara yin Ibadah, a samu dacewa sannan kuma biki da murna su biyo baya.

Da ma ta ƙarshe ita ce waɗannan gwalagwalan kwanaki wanda ko da mun yi wasa a baya zamu wanke kan mu a cikin su.

Mu riƙa ƙoƙarin tashi daga bacci mu yi sallar nafila, tahajjud kuma mu samu lokacin karatun Alƙur’ani. A rage amfani da waya, a bar jin kaɗe-kaɗe, a nisanci duk wani abu da zai kawo shagala ko kuma ya kai mu ga aikata zunubi.

A rika yawan tasbihi, salatin Annabi da istigifari. A daure da salloli akan lokaci sannan a rika yin addu’o’i masu amfani.

A dage da yi wa ƙasa addu’a, Allah ya fitar mu daga irin halin da muke ciki, ya saukaka mana al’amura. Idan da hali ma akan iya shiga ittikafi, a keɓance da bautar Allah maɗaukaki, a wannan kwanaki goman na ƙarshe. Da neman dacewa da daren Lailatul Ƙadari.

Allah ya sa mu dace. Amin.

Sai dai kuma da yawan mu matasa ba mu damu da irin albarkar da take cikin wannan kwanaki na ƙarshe ba, za mu yi sallarmu ne fisha mu gama kamar yadda muke yi a koyaushe mu tashi mu yi tafiyarmu. Haka ma idan lokacin buɗe-baki ya yi, sai ya zama gabaɗaya ta abinci ake ba ta albarkar azumin da muka yi ba. Sai kawai a zurfafa cin abinci ba tare da addu’a ba, sannan kuma ga tsananin mita akan azumin da muke. Yau azumi ya yi wahala, wasu su na azumin ma amma burinsu kawai su kushe azumin, wanda gabaɗaya ba shi da kyau, kuma ba shi da amfani.

Haka sai wannan wata mai albarka ya zo ya tafi ba a tsinana komai ba, ana yau za ayi, gobe za a canja har dai ya zama kuma an zo goman ƙarshe. Anan wasu masu ragowar hankalin su kan nutsu su yi wa kansu faɗa su fara gyarawa, wasu kam haka zai zo ya tafi ba su waiwayo ba. Allah ya raba mu da asara. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *