Kwankwaso ya buɗe ofishin jam’iyyar NNPP a shiyoyi uku dake jihar Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya a babban zaɓen dake tafe na shekara ta 2023 a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya buɗe sabbin ofisoshin jam’iyyar a Jihar Katsina.

Kwankwaso ya samu tarba daga ɗaruruwan magoya baya a ofisoshi uku da ya ziyarta, wato na Katsina, Malumfashi da kuma shiyyar Funtuwa.

Ya kuma samu tarba daga jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar ta NNPP a Jihar Katsina Eng. Nura Khalil da kuma shugaban Ƙungiyar Kwankwasiyya Organization na Jihar Injiniya Muhammd Kabir Musa Funtuwa.

An ƙaddamar da babban ofishin jam’iyyar a gaban ɗimbin magoya bayan jam’iyyar da suka fito daga ƙananan hukumomin jihar a kan hanyar IBB wato hanyar Katsina zuwa Kano a yayin da aka buɗe na shiyyar Funtuwa a kan hanyar Funtuwa zuwa Zariya.

Da yake jawabi bayan ƙaddamar da ofishin shiyyar Funtuwa, Injiniya Muhammad Kabir Musa Funtuwa, ya yaba wa madugun jam’iyyar bisa amincewa da ya yi na zuwa Jihar Katsina ya kuma buɗe ofisoshin jam’iyyar da kansa.

Daga nan sai ya yi wa ɗan takarar shugabancin ƙasar gami da sauran masu fafutukar ganin an zaɓe su a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar fatan samun nasara a manyan zaɓuka dake tafe na shekarar 2023.

Shugaban ƙungiyar kwansiyya na jihar ya kuma bayyana fatan sa na ganin ɗan takarar na su ya kai labari don kawo ɗumbin ayyukan cigaba a ƙasar nan da suka haɗa da fannin ilmi, lafiya da dai sauran su.

Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu rakiyar Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa Buba Galadima da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Ƙaddamar da ofisoshin a shiyyoyi uku na jihar na zuwa ne kwanaki kaɗan kafin ranar fara yaƙin zaɓe da hukumar zave mai zaman kanta ta lamunce wa jam’iyyun siyasa a ƙasar nan da ke fatan ganin an fafata da ‘yan takararsu wajen neman ɗarewa muƙamai daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *