Kwankwaso ya lallasa Tinubu da Atiku a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu 2023,

Daga ƙarshe dai an kammala tattara sakamakon na ƙananan hukumomin 44 na jihar Kano.

Don haka an ayyana ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kano, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da ƙuri’u 479,938.

Jihar Kano ta na da masu kaɗa ƙuri’a kusan 5,792,848 wadanda aka yiwa rijista, ya yinda aka tantance masu kaɗa ƙuri’u 1,769,525, kamar yadda sakamakon da Farfesa Lawan Suleiman Bilbis mataimakin shugaban jami’ar Usman Danfodiyo ya sanar a cibiyar tattara sakamakon zaɓe da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana.

A sakamakon ƙarshe na ƙuri’u inda jimillar masu kaɗa ƙuri’a 1,746,410 suka kaɗa ƙuri’a, Kwankwaso ya samu ƙuri’u 997,279 inda ya doke Tinubu wanda ya samu kuri’u 517,341; Atiku Abubakar na PDP, wanda ya samu ƙuri’u 131,716 da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu ƙuri’u 28,513.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Kwankwaso wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne a karo na biyu, ya samu nasara a kananan hukumomi 36 daga cikin 44 yayin da Tinubu ya lashe sauran ƙananan hukumomi 8.

Ƙananan hukumomin da Kwankwaso ya lashe su ne: Garun Malam, Rimin Gado, Kibiya, Kura, Gezawa, Minijibir, Warawa, Gabasawa, Sumaila, Rogo, Dawakin Tofa, Ƙaraye, Dambatta, Dawakin Kudu, Tofa, Madobi, Bunkure, Bebeji, Rano, Ajingi, Albasu, Wudil da kuma Tarauni.

Sauran sun hada da: Gaya, Ungogo, Ƙiru, Garko, Tsanyawa, Tudunwada, Kumbotso, Kano Municipal, Takai, Fagge, Nasarawa, Gwale da Dala.

Ita kuwa APC ta yi nasara a Makoda, Kunchi, Ɓagwai, Doguwa, Bichi, Gwarzo, Kabo da kuma Shanono.

Jimillar ƙuri’un da aka kaɗa a rumfunan zaɓe sun kai 1,702,005 yayin da ƙuri’un da aka ki amincewa dasu suka kai 44,405 wanda ke nufin akwai jimillar 1,746410.