Kwara: An samu hatsaniya tsakanin Musulmi da Kirista saboda hana ɗalibai amfani da hijabi

Daga UMAR M. GOMBE

An samu rashin jituwa biyo bayan yadda iyaye mabiya addinin Kirista suka hana ɗalibai mata Musulmi shiga makarantar Sakandaren Baptist a babban birnin jihar Kwara, Ilori.

Bayanai sun nuna cewa sakandaren na daga cikin goma da tun farko gwamnati ta rufe don hana fitina yayin da jihar ta bada dama ga mata musulmi da ke sha’awa su sanya hijabi in za su tafi makaranta.

Gwamnatin ta nuna hakan shi ne zai tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin jama’ar jihar.

Dakatar da ɗaliban da kiristoci suka yi, ya jawo ɗauki ba daɗi na jifa da duwatsu da kujeru kan juna har wasu suka samu raunuka.

Jihar Kwara na daga jihohi masu yawan mabiya addinin Musulunci da kuma Kirista a Arewacin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *