Kwararowar makiyaya: Ana zaman ɗarɗar a arewacin Jihar Bauchi

*Sun fara dirar mikiya a gonaki ɗauke da bindigogi, inji tsohon ɗan majalisa
*Mu na sane da su, cewar Hakimin Gamawa
*Mun fara kama waɗanda suka yi ta’adi – Rundunar ’Yan Sanda

Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi

Manoma mazauna Ƙaramar Hukumar Gamawa da wasu sassan arewacin  Jihar Bauchi da Jigawa na cikin zaman zulumi da ɗarɗar, saboda bayyanar wasu Fulani makiyaya da babbobinsu, waɗanda suka fito daga wasu yankuna da ake fama da rashin tsaro a Nijeriya, musamman Arewa maso Gabas da ma Jamhuriyar Nijar, inda mazauna yankin na arewacin Bauchi da jihar Jigawa ke ƙorafin makiyayan na tura dabbobinsu dubbai su na cinye musu amfanin gona da ba a kai ga kammala girbewa ko kwashewa zuwa gida ba.

Idan za a iya tunawa, a jaridar ranar 22 ga Oktoba, 2021, Blueprint Manhaja ta ruwaito yadda aka ga ɓullar wasu makiyaya da suka yi gudun hijira daga ƙasashen yankin Kudancin Nijeriya zuwa Jigawa, inda suka fara gararamba har a Dutse, Babban Birnin Jihar.

Alhaji Buba Yarima, Matawallen Gamawa kuma tsohon ɗan majalisar dokokin yankin lokacin mulkin Shagari, ya bayyana yadda a yanzu makiyaya suka fara yin mamaya a kan iyakar Bauchi da Jigawa a cikin hirarsa da manema labarai a Bauchi. Ya ce, ana zaman ɗarɗar a yankin, saboda “a lokaci guda sai dubban shanu da dabbobi su yi dirar mikiya a gonar mutum su cinye komai,” inji shi. 

Ya ƙara da cewa, wani lokacin kuma da rana suke zuwa, inda ake kai ruwa da masu gona suna jan amfaninsu dabbobi na shiga su na ci, kuma makiyayan suna ɗauke da bindigogi a hannunsu.

Buba Yarima Gamawa ya ci gaba da cewa, “shanun bakwaloji ne wasu farare wasu jajaye, haka za a gan su ɗaruruwa sun fito daga yankin Borno da Yobe ko daga Zamfara ko Sakkwato ko Jamhuriyar Nijar, kuma duk gonar da suka shiga sai dai su bar mai gonar da kuka.”

Don haka ya buqaci gwamnati ta kai ɗauki, don ganin ba a samu asarar rai ko matsala tsakanin manoma da makiyayan ba, saboda abin da ke faruwa na tada hankalin manoma sosai.

Wakilin Blueprint Manhaja ya tuntuɓi Mai Girma Hakimin Gamawa, Alhaji Adamu Abdulkadir, wanda ya tabbatar da zuwan makiyayan, amma ya ce, a wuri ɗaya aka samu matsalar kuma tuni hukuma ta shiga tsakani, an magance lamarin.

Ya qara da cewa, “da ma duk shekara makiyayan suna sanar da su kafin su zo yankin, amma saboda rashin zaman lafiya a wasu yankuna, bana yawansu ya ƙaru.”

Don haka suka tashi tsaye tare da jami’an tsaro suka shiga lamarin aka daidaita komai. Saboda haka suke jan hankalin manoma su kwashe amfaninsu zuwa gida. Su ma masu noman kankana da guna su kammala gonakinsu, kamar yadda aka saba don guje wa tashin hankali.

Shi ma Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce, amma rundunar tare da haɗin kan sauran hukumomin tsaro da ‘yan banga a yankin sun shiga cikin lamarin, kuma duk waɗanda suka yi ta’adi an kama su sun biya.

Don haka sai ya buƙaci manoma da su kwashe amfanin gonar su kuma su guji ɗaukar doka a hannunsu, ta hanyar isar da kukansu ga jami’an tsaro idan an taka musu wani haƙƙi, domin a shirye suke wajen ganin sun bi haƙƙin kowa.